Mene ne ƙaho da kuma tsakiya a Hausa? Kuma waɗanne cututtuka ake yi wa magani da su?
Kaho/ Hijama: Waata hanya ce da ake neman lafiya daga cututtuka da suka damu ɗan’adam. Kaho ya samo asali tun iyaye da kakanni kuma ana yin shi musamman a kasar Hausa.
Yadda Ake Kaho.
Shi dai kaho ana yin shi ne a gargajiyance ta hanyar amafani da kahon dabba wanda aka sarrafa, musamman ma kahon kananan dabbobi kamar raguna, awaki da tumaki. Akan yanka kahon a goge shi daidai yadda zai ba da damar kafa shi a cikin mutum. Idan za a yi wa mutum Kaho, wanzami zai dasa kahon a daidai inda ke da tararren mataccen jini a jikin mutum. A na amfani da aska domin yin tsaga a daidai wajen kafin a sanya kahon a rufe, sai kuma a sanya baki a saman kahon wanda yake da dan rami karami, sai wanzami ya sa bakinsa a kan ramin yayi ta hurawa yana zuqowa har sai mataccen jinin ya fito duka.
Kaho ya kasance hanya mafi sauki wajen yaki da cututtuka wadanda ma ba a san suna wanzuwa a jikin dan’adam ba. Binciken likitanci na zamani ya tabbatar da cewa yin kaho kariya ce daga kamuwa da hawan jini ko kuma ciwon da suke da alaka tsarin kwayoyin halitta da ciwukan da suke da alaka da Zuciya. Bugu da kari har matsalolin kwakwalwa za a iya magance su ta hanyar yin kaho.
Kaho ya samo asali ne tun shekaru dubbai da suka gabata a kasar Sin, inda suke amfani da shi wajen maganin matsalolin jini da ciwon jiki.
Mece ce kaciyar mata?
Duk da cewa an fi yin kaciyar mata a wasu kasashen Afirka da gabas ta tsakiya 30, a wasu kasashen Asiya da Latin Amurka ma ana yi wa mata kaciya.
Haka ma tsakanin al’ummomi baki mazauna yammacin turai.
Matan da ake yi wa kaciyar na samun rauni ko tabin hankali daga baya, kamar yadda Bishara Sheikh Hamo daga yankin Borana a lardin Isiolo na kasar Kenya ta bayyana.
“An yi mini kaciyar mata ina ‘yar karama,” in ji ta. “A lokacin kakata ta fada mani cewa abu ne da ake yi wa kowace ‘ya mace domin yana tsarkake su.”
Sai dai ba a fada wa Bishara cewa kaciyar na iya haifar mata da rikicewar al’ada da matsalar mafitsara da yawan kamuwa da cutuka na tsawon rayuwa ba.
Kaciyar mata ita ce yankewa ko cire wani bangare da ke wajen al’aurar mata.
Ta kunshi yanke dumbaru, kuma Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana ta a matsayain “duk wani abin da ke haifar da rauni ga al’aurar mace ta wata hanya ba ta likitanci ba.”
Kaciyar mata hadari ce ga mata kuma tana yin illa ga yadda mata ke daukar kawunansu.
Kaciyar mata iri hudu ce:
Nau’i Na Farko: Cire dumbaru gaba daya tare da fatar da ke kwaye da ita.
Nau’i Na Biyu: Cire dumbaru ko bangarensa tare da cire fatar da ke zagaye da farjin mace ta ciki.
Nau’i Na Uku: Yankewa tare da sauya wa fatar farji yanayi. Ya hada da dinki ta yadda ake barin wata karamar kofa.
Wannan nau’i na da tsananin zafi da tashin hankali tare da haifar da cuta ga fata: Ana toshe kofar farji da mafitsara sannan a bar wa matan wata ‘yan kofa domin yin fitsari da fitar jinin al’ada.
Wani lokaci kofar kan yi kadan har sai an kara girmanta domin a iya saduwa da macen ko ta iya haihuwa – wanda yakan haifar da matsala ga jariri da mahaifiyarsa.
Nau’i na hudu: Ya kunshi sauran nau’ikan da aka ambata a baya da suka hada da hudawa da yankawa da gogewa ko kona dumbaru da sashen al’aurar mace.
Me ya sa ake yi?
An fi ambaton al’ada da addini da mummunar fahimta fiye da lafiya a matsayin hujjar yi wa mata kaciya da sunan hanyar kare budurcinsu domin su samu auruwa da kuma kara masu ni’ima wurin saduwar aure.
A wasu wuraren kaciyar mata wata al’ada ce da ake yi yayin shiga matakin balaga da kuma a matsayin sharadin aure.
Duk da yake babu wata fa’ida a likitance da kaciyar mata ke da ita, al’ummomin da ke yin ta sun yi amannar cewa akwai bukatar yi wa mata ita, suna kuma kallon matan da ba a yi masu ba tamakar marasa lafiya ko marasa tsarki ko kamala.
Galibin matan ba da son ransu ake masu kaciya ba. Kwararru a fannin lafiya a duniya na daukar kaciyar mata a matsayin cin zarafi da tauye hakkin mata.
Haka kuma ana daukar ta a matsayin cin zarafin kananan yara a duk sadda aka yi wa yara ita.
A ina ake yin ta?
Yawancin matan da Asusun Yara na MDD UNICEF da Hukumar Lafiya ta Duniya WHO suka tambaya sun ce al’ummomin da suka fito na ganin yin magana game da kaciyar mata wani alkaba’i ne, shi ya sa ake kiyasin al’kaluman da aka bayar.
Wani lokaci matan ba sa yin magana a fili game da ita saboda gudun suka daga jama’a.
A wasu lokutan kuma – a wuraren da aka haramta yi wa mata kaciya – tsoron gurfanar da iyalai ko al’ummar a gaban shari’a ne ke hanawa.
MDD ta yi kiyasin cewa ko da yake an fi yi wa mata kaciya a kasa 30 a nahiyar Afirka, a yankin gabas ta tsaikiya da wasu kasashen Asiya da Latin ma ana yi.
Ana kuma yi a al’ummomin baki mazauna yammacin Turai da Arewacin Amurka da Australi da da kuma New Zealand.
Rahoton binciken da UNICEF ta gudanar a kasashen Afirka 29 da gabas ta tsakiya ya nuna cewa ana yawan yin kaciyar mata, duk da cewa 24 daga cikin kasashen sun yi dokokin haramta yin ta.
A kasashe irin Birtaniya inda aka haramta kaciyar mata, wata kwararriya kuma lauya Charlotte Proudman ta ce ana yawan yin ta ga kananan yara, kuma yana da matukar wuyar a gano domin yaran ba su fara zuwa makaranta ba ko kuma ba su da wayon da za su iya kai rahoto.