Mecece Giba (Gulma?), ya hukuncin yin ta a Musulunci?
GIBA/GULMA DA HUKUNCIN YIN TA A MUSULUNCI.
Giba, wadda da Hausa ake kiran ta da ‘Cin naman mutum’ wato yi da mutum alhalin ba ya nan, haramun ce, domin musulunci ya yi hani da aikata duk abin da zai taɓa mutuncin wani, abin da ba ka so, to kai ma ka da ka yi wa wani shi, ba ka so a yi gibar ka, to kai ma kada ka yi gibar wani, domin lallai ita tana da girman zunubi a wajen Allah.
Gulma hanya ce ta tozarta mutane wadda duk mai yin ta ƙarara yake shi ba mutumin kirki ba ne don zai iya yin gulmar kowa musamman a ce ya maida ta sana’arsa. Sannan gulma tana ragewa mai yin ta daraja da girma a gurin mutane musamman idan aka fahimci mutum shi magulmaci ne. Kuma gulma tana haɗa faɗa. A addinin Musulunci gulma babbar zunubi ce wanda har sai mutum ya nemi yafiyar wanda ya ci namansa, sannan kuma ya nemi yafiyar Allah Subhanahu Wata’ala.
Gulma, giba, yi da mutum, duk sun yawaita a wannan zamani, kuna zaune da mutane a tare, da zarar ka tashi za su fara yin gulmar ka, ko kuma wani zai zo wucewa sai kawai su hau yin gulmar shi, sun ɗauka cewa Allah ba zai tambaye su duk abin da suka kasance suna aikatawa ba.
“An karɓo hadisi daga Abu-Hurairata Allah Ya ƙara masa yarda yace: Manzon Allah ﷺ, ya ce: Shin kun san mece ce giba kuwa? Sai ya ce: To ita ce ambaton ɗan-uwanka da abin da ba ya so, idan ya kasance abin da ka faɗa a kansa ɗin gaskiya ne, to ka yi gibarsa, idan kuma abin da ka faɗa ba haka ba ne, to haƙiƙa ka yi masa buhtani, (ka yi masa ƙage) Sahih Al-Jam’i (86).
Daga cikin tushe na zaman lafiya da ka’idoji na tsira akwai kiyaye harshe daga sharrace -sharrace da laifuka da shaidar zur da karya da kage. Allah Madaukakin Sarki ya ce:(Ba ya lafazi da wata magana face tare da shi akwai mai tsaro halartacce) Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: (Wanda ya kasance yana imani da Allah da ranar lahira to ya fadi alheri ko ya yi shuru). An yi ittafaki bisa ingancinsa. Kuma Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: (Wa zai lamunce mini harshensa da farjinsa sai na lamunce masa Aljannah.) Bukhari ne ya ruwaito.
Ma’abota ilimi suka ce: “Ba ya dacewa ya yi magana sai idan akwai alheri a maganar, wato ita ce wacce maslahar yin ta ta bayyana, duk wanda ya yi shakku bisa maslaharta to ya yi shiru.”
Allah madaukakin sarki ya ce “Kada wasu sashinku su ci naman wasu.” Hakika Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya fassara da fadinSa (Ko kun san mece ce gibah? Sai suka ce Allah da ManzonSa ne suka fi sani, sai ya ce shi ne: Ambaton dan’uwanka da abin da ba zai so ba, sai aka ce to idan ga dan’uwan nawa akwai abin da nake fadi tattare da shi fa? Sai ya ce: Idan har akwai tare da shi abin da kake fadi to hakika ka ci namansa, to idan babu tare da shi abin da ka ke fadi to ka yi masa kage.) Muslim ne ya ruwaito shi.
Lallai giba tana kai mutum ga halaka, an yi alkawarin ukuba mai girma ga mai yin ta da sakayya mai radadi Allah Madaukakin Sarki ya ce: “Da wadanda ke cutar da muminai maza da muminai mata ba tare da wani abu da suka aikata ba to hakika sun riki kage da laifi bayyananne.)
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace :
“A yayin da aka yi Mi’iraji da ni zuwa sama na hadu da wasu mutane suna da faratu na karfe suna yagunar fiskokinsu da kirazansu, sai na ce su wane ne wadannan ya Jibrilu? Sai ya ce: Wadannan su ke cin naman mutane suna taba mutuncinsu.” Abu Dawuda ya rawaito, Ibnu Hajar da waninsa suka ce hadisi ne Hasan, Ibnu Muflih ya ce: Isnadinsa ingantacce ne.
Don haka ya haramta ga musulmi da ya bada dama a yi gulmar wani a gaban shi ko ya saurari hakan ko ya karanta, sai dai ma ya zama wajibi a gare shi ya yi hani ga mai gulman, kamar yadda ka’idoji na sharia ya gindaya.Allah Madaukakin Sarki ya ce:
“Kuma idan ka ga wadanda suke kutsawa a cikin ayoyinMU to ka bijire daga gare su har sai sun kutsa a cikin wani labari da ba shi ba, kuma lallai imma shaidan ya mantar da kai to kada ka zauna a bayan tunawa tare da mutane azzalumai).
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace:
“Duk wanda ya kare mutuncin dan’uwansa musulmi to Allah ma zai kare fiskarsa daga wuta ranar Alkiyama.” Tirmizi ne ya rawaito ya ce hadisi ne hasan Ibnu Hajar shi ma ya ce Hadisi ne Hasan.
WALLAHU TA’ALA A’ALAM.