Mece ce Sallah, da kuma matsayinta a Musulunci.?
Sannan ya matsayin wanda ya tsaida ta kamar yadda Allah ya umurta.?
Sannan menene hukuncin wanda ya tozarta Sallar?
Sallah ita ce ibadar nan da falalar ta ta cika kunnuwan halittu, saboda abin da aka tanadar wa masu kiyaye ta. An rawaito daga Abu Umamata Allah Ya ƙara yarda a gare shi, cewa, Manzon Allah (S.A.W.) ya ce:
“Duk wanda ya fita daga gidansa yana mai tsarki zuwa sallar farilla, to zai samu ladan wanda ya yi harama da hajji, wanda kuma ya fita zuwa sallar nafila babu abin da ya tashe shi sai ita, to zai samu ladan wanda ya yi Umara, kuma sallar da aka yi bayan wata sallar, alhali babu yasasshiyar magana a tsakanin su, za a rubuta ta a cikin illiyyuna.
Haka nan Annabi mai tsira da aminci ya ce: “Sallah ita ce mafificin abu, don haka duk mai son yawaita ta, to sai ya yawaita.” Ɗabarani ne ya rawaito.
Muhimmancin sallah ya ƙara bayyana ne cikin kasancewarta an saukar da ita daga ɓirɓishin sammai bakwai, ba tare da an aiko ta hanyar saƙo ba, da kuma kasancewarta mai sadarwa tsakanin bawa da Ubangijinsa. Sallah ta kasance ita ce abin faranta ran masana Allah, kuma hasken zukatansu, ga ta kuma tana hani ga barin alfasha da mummunan aiki kamar yadda Allah Ya faɗa cikin suratul Ankabut.
“Haƙika sallah tana hana alfasha da mummunan aiki.”
Sallah ita ce maraba tsakanin kafirci da imani, domin Jabir ya ruwaito cewa, Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya ce, “Haƙiƙa abin da ke tsakanin mutum da kafirci ba wani abu ba ne face barin sallah.” Muslim ne ya rawaito shi.
Haka nan, an karɓo daga Buraida ya ce: Na ji Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama yana cewa: “Alƙawarin da ke tsakaninmu (Mu musulmai) da su (kafirai) shi ne sallah, duk wanda ya bar ta haƙiƙa ya kafirta.” Hadisi ne kyakkyawa ingantacce.
Masu tsayar da Sallah da yin ta a cikin jama’a kamar yadda Allah Ya umarta suna da cikakken matsayi mara algus, domin kuwa Muslim ya rawaito daga Abu Huraira ya ce: “Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya ce, “Sallah a cikin jama’a ta ɗara sallar mutum a cikin gidansa, da sallarsa a kasuwarsa da daraja ashirin da ɗoriya, dalilin haka shi ne idan ɗayansu ya yi alwala, ya kyautata alwalar, sannan ya zo masallaci, babu wani abu da ya zaburar da shi sai sallah, kuma ba ya nufin komai face sallah, ba zai yi taku ɗaya ba face an ɗaukaka masa daraja ɗaya da shi. Kuma an sarayar masa da laifi ɗaya da shi, har sai ya shiga Masallaci. Kuma idan ya shiga Masallaci zai zamo cikin ladan sallah matuƙar sallah ce ta tsare shi, kuma Mala’iku suna yin addu’a a bisa ɗayanku matuƙar ya kasance a mazauninsa da ya yi sallah a cikinsa, suna cewa: “Allah ka gafarta masa, Allah ka karɓi tubansa, matuƙar bai cuci wani ba a cikinsa, matuƙar alwalarsa ba ta karye ba.”
Sai dai duk da hakan za ka ga da yawa daga cikin Musulmi suna sakaci cikin ba da wannan farilla mai girma, suna tozarta ta, suna yi amma ba sa kyautata ta, suna caccaka ta caccakar hankaka, ba sa nutsuwa, kuma ba sa tuna Allah a cikin ta sai kaɗan. Sun manta ita ce farkon abin da Allah Ya wajabta a ibadodi. Kuma ita ce farkon abin da za a yi wa bawa hisabi a kansa ranar alƙiyama. Kuma ita ce ƙarshen wasiyyar da ma’aikin Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya yi wa al’ummarsa wasiyya da shi a yayin rabuwar shi da duniya. Inda a lokacin da zai cika ya ce: “Ina jaddada muku lamarin sallah! Ina jaddada muku lamarin sallah da kuma lamarin bayinku.” Ahmad da Abu Dawud da Ibnu Majah suka rawaito shi.
Don haka abu ne sannane azaba mai raɗaɗi ta tabbata ga masu tozarta sallah a ranar Lahira.
Mu kiyaye sallah ta hanyar ba da rukunanta, da sharaɗanta da wajibanta,sannan mu cika ta ta hanyar aikata mustahabbanta, domin sallah ita ce jigon Addini, kuma babu addini ga wanda babu sallah a gare shi. Allah Subhanahu wata’ala a cikin suratul Baƙara ya ce:
“Ku kiyaye salloli, da kuma tsallar tsakiya.”