Mun sani ana yin azumi a wannan wata na Rajab da ake kira da azumin tsofaffi. Wace falala ce a cikin azumtar watan?
Watan Rajab wata ne daga cikin jerin watannin Musulunci, wanda Musulmai suke girmamawa, ta hanyar yin azumi a cikinsa, wanda mu a hausance muna kiran wannan azumi da Azumin Tsofaffi.
Toh amma a fahimtar addini, ba kowa ne ke keɓance watan Rajab da azumi ba, saboda bai zo a Sunna ba, kawai dai idan mutum zai yi azuminsa toh kawai ya yi, amma ba wai da niyyar don wannan watan ba.
Prof. Mansur Sokoto ya taɓa wani rubutu a kafafen sadarwa, inda ya ce “Babu abin da ya inganta game da falalar watan Rajab sai kasancewar sa cikin watanni huɗu masu alfarma, Saboda haka mu kama kanmu daga saɓon Allah a cikinsa, mu kuma yawaita ibada a cikinsa.”
Prof. Mansur Sokoto ya cigaba da cewa “Amma, duk wata addu’a ko sallah ko azumi aka keɓe shi da watan Rajab to bai inganta daga Manzon Allah sallallahu alaihi wasallam ba, kuma yin sa da wannan niyya yana cikim bidi’a.”
Malam Abdulhadi Isah Ibrahim ma a shafinsa na facebook ya taɓa rubuta cewar “Watan Rajab wata ne mai falala saboda Manzon Allah ya sanya shi daga cikin watanni huɗu waɗanda Allah ya haramta yaƙi da saɓo acikin su, a Suratut Taubah aya ta 36, akwai watanni hudu masu alfarma sama da sauran watanni, sune ‘Zul-qa’adah, Zul-hijjah, Al-muharram da kuma Rajab (na ‘yan Qabilar Mudar).
Babu wani Hadisi da ya tabbata daga Manzon Allah cewa ana yin azumi na musamman a watan Rajab bayan azumin Litinin da Al-hamis da kuma azumi uku Wanda ake yi acikin kowane wata (azumin Nafila), bayan Waɗannan babu wani azumi da aka ce ya inganta ayi a watan Rajab, keɓe shi da wasu salloli a dararen sa bidi’a ce, keɓe shi da wasu azumi bidi’a ce.
Ibnul Qayyim al-jauziy acikin littafin sa “Manarul Muniyf” a shafi na 96 ya ce “Duk hadisan da suka zo suka ce Annabi ya ce ayi azumi ko salloli na musamman a watan Rajab Hadisan ƙarya ne, Duk wata ibada da aka ware ta saboda watan Rajab bidi’a ce, magabata basu San da ita ba.’
Imam Sayyid Sabiq acikin littafinsa ” Fiqhus Sunnah” a mujalladi na ɗaya shafi na 383 yana cewa “Bayan azumin kwanaki 3 a duk wata, da na Litinin da Al-hamis a watan Rajab, to babu wata ibada da Manzon Allah ya ce ayi sama da haka.’
Shaikhul Islam Ibni Taimiya ya ce “Hadisan da aka ruwaito su cewa wai Annabi ya ce ga falalar watan Rajab na musamman, Hadisan wasu mutane ne suka zauna suka rubuta su suka yi karya wa Manzon Allah (S.A.W) shi bai faɗa ba bai ce ba.’
Don haka in kana son tsira ka tsaya kaɗai akan abin da annabi Muhammad (S.A.W) ya tsaya..”
Sosai wannan fahimta ta waɗannan Malamai bisa ga hujjojin da suka dogara da su suka bayyana matsayin rashin hallaccin keɓence Watan Rajab da yin azumi.
A wata fahimtar kuma wasu Malaman suna nuna halaccin yin azumi domin watan Rajab, inda har suka kawo wasu Falaloli masu tarin yawa dangane da yin azumin.
Shafin NURUL ILMIL ISLAM da ke facebook sun yi wani rubutu mai ɗauke da falalar yin azumin watan Rajab kamar haka:
“Duk wanda ya azumci Ranar Farko ta watan Rajab, wannan Azumin yana dai-dai da azumin wata guda/daya (1).
Duk wanda Ya azumci kwana uku (3), Alhamis Juma’a da kuma Asabar, Allah zai rubuta masa ladar Ibadar shekara Cis’in (90).
Jahannama tana da Ƙofofi bakwai (7),
Duk wanda ya yi azumin kwana bakwai (7), a cikin watan Rajab, za’a rufe masa Ƙofofin Jahannama, sabida Azumi bakwai (7) da ya yi.
Duk wanda ya yi azumin kwana takwas (8), za’a buɗe masa ƙofofi takwas (8) na Aljannah ya shiga ta Qofar da yake so.
KUMA BA LALLAI SAI KA JERA SU A JERE BA, MISALIN YANDA ABUN YAKE:-
Idan azumi 7 ko 8 ko 10 ko 15 ko 18, za ka yi, daga ciki duk wanda ka zaɓa, ba lallai sai ka jera su ba, za ka iya yin uku 3, sai ka huta bayan kwana biyu (2) sai ka ƙara yi, abin da ake buƙata, kafin watan ya Qare ka hada adadin da ka dauki niyya za kayi, inma 7 ko 8 ko 10 ko 15 ko 18.”
Wannan falalar ta watan Rajab da wannan shafi suka kawo, ta nuna fahimtar wasu Malaman na halaccin keɓence watan Rajab da Azumi.
Dan haka dai saɓanin Malamai Rahama ne kamar yadda ake faɗa. Ya rage ga mu mabiya, idan halacci mutum ya ɗauka, toh zai iya yi, idan kuma mutum ya bi Malamai masu ganin bai halatta a keɓe watan Rajab da Azumi ba, toh ba sai ya yi ba.
Allah shi ne Ma fi sani.