Me ya kamata mutum ya tanada idan zai haɗa sabulun gyaran jiki, wanda ba zai kawo illa ga lafiyar fata ba.?
Yadda ake haɗa sabulun gyaran jiki mai kyau wanda ba zai kawo illa ga fata ba .
Yadda Uwargida za ta gyara jikinta ta fito tana ƙyalli saboda sabulu mai inganci da ta haɗa kuma take yin wanka da shi:
Abubuwan da ake bukata domin haɗa wannan sabulu sun hada da:
Sabulun salo,
Sabulun wanka,
Majigi,
Man kwakwa kadan,
Man zaitun shi ma kadan,
Lemon tsami ki dan yanki kadan shi ma amma idan kin san ba ya saka ki kuraje a fuska. Saboda wasu idan suka yi amfani da lemon tsami yana saka su kuraje a fuska,
Jar kanwa kadan ita ma,
Alobera kamar guda uku, Ƙwanduwar ƙwai kamar uku ita ma.
Yadda ake hada su:
Za ki dauki sabulun salo ki saka shi a cikin turmi, sannan ki dauko sabulun wanka shi ma ki saka shi a cikin turmi, ki hada su ki ta dakawa har sai sun daku wato sun hade jikinsu sun zama abu daya, to shi ne sun daku, sannan ki kawo duka abubuwan da muka ambata a farko ki zuba su a cikin turmin, amma ki dan rage man kwakwa wanda idan kin zo curawa za ki dangwala hannunki a ciki ki hade su gaba daya ki yi ta dakawa har sai sun hade, daga nan sai ki fara cura shi.
Yadda za ki cura za ki gutsiri sabulun salon a hannunki sai ki dan lakuci man kwakwar a hannunki, dama mun ce za ki rage man kwakwa saboda curawa to wannan wanda kika rage shi za ki yi amfani da shi saboda kar sabulun ya kama miki hannu, kina curawa haka kina mulmule shi. To wannan sabulun shi ne zai zama sabulun wankanki a koyaushe, kafin ki shiga wanka za ki dan iya shafa shi a fuskarki kamar na minti biyar haka, za ki ga yadda fatar jikinki za ta yi kyau cikin sati biyu da yardar Allah. Za ki dinga walwali da sheki, kuma fatarki za ta yi taushi da sulɓi in sha Allah. Saboda dukkan abubuwan da aka haɗa domin yin wannan sabulu abubuwa ne na gargajiya masu kyau, babu wani kemikal a ciki wanda zai iya taɓa lafiyar fata.
Wannan shi ne yadda ake hada sabulun gyaran jiki wanda ba ya illata fata.