Sanannen abu ne cewa ana yawan satar kayan lefen amare, to amma me ya sa?
Satar kayan Amarya ba sabon abu bane a cikin al-ummah, domin an sha wayiwar gari a ga ba lefe, ko kuma wasu daga cikin kayan ɗakinta irinsu TV d.s, kuma a rasa ɓarawon na gida ne ko na waje. Dalilan da ke sanyawa a yi ma Amarya satar kuma guda uku ne, a tawa fahimtar amma.
Sakacin ita amaryar, ko kuma danginta, dalilina na faɗin haka shi ne, dukkansu suna da gudunmawar da zasu bada wurin killace kayan amaryar a lokacin da ake ganiyar hidimar bikin, musamman danginta, haƙƙin ya fi rataya a kansu wurin kula da inda ya kamata a adana ma amarya kayanta, da kuma lura da masu shige da fice a inda kayan su ke, don haka a cikin hidimar biki sakacin dangin amarya ne ke sanyawa a yi mata sata, tunda haƙƙin kula da komai yana a wurinsu. Idan kuma bayan biki ne, toh sakacin amarya ne ita da Ango, saboda haƙƙin kula da komai na gidan yana a wurinsu, don kuwa yana da kyau su fara lura da yanayin unguwarsu, su ga shin akwai jama’a? Sannan suna da tsaro a unguwar? Da sun lura da wannan, sai su san irin matakin da zasu ɗauka idan suna gida, da kuma idan basa nan.
Dalili na biyu kuma shi ne ƘARYA: irin wannan ƙaryar kuma tana fitowa ne daga wurin Ango, dalilina shi ne, an sha samun Angon da ya haɗa baki da wasu a shigo a sace kayan amarya, musamman lefe idan bata nan, wani lokacin angon ne ma da kansa ke yin wannan aika-aikar, sai a fake da ɓarayi ne suka shigo suka ɗauki kayan. Babban dalilin yin haka kuma shi ne, don a maida kayan inda aka yo hayarsu, ko kuma biyan bashin da ya ci lokacin hidimar bikin.
Dalili na Uku kuma shi ne Ƙaddarar Ubangiji: Wannan dalili kuma ya shafe dukkanin waɗancan, ko kuma in ce ma tare suke tafiya, domin ko da sakaci, idan Allah bai ƙaddara faruwar wani abu ba, toh ba zai faru ba. Sannan idan Allah ya ƙaddara faruwar abin, ko da an kula sosai, toh fa ba mahani, don kuwa sai ya faru.
Waɗannan su ne dalilan da suke sa ayi ma amarya sata waɗanda ni na gano, na san ba za a rasa ƙarin wasu ba. Da fatan Allah ya kyauta Am
iiiiin.
Sannu da ƙoƙari.