Ya ya ake yin wainar shinkafa (Masar Bauchi) da miyar taushe?
YADDA AKE MIYAR TAUSHE
Uwar gida zata tanadi abubuwa kamar haka:
1. Cefane (Tattasai, Tumatir, Attarugu, Albasa)
2. Nama.
3. Mai (Fari ko ja)
4. Alaiyyahu ko Ugu ko shuwaka.
5. Spices.
6. Kabewa
Uwargida zata yanka cefane haɗe da ƴar tafarnuwa da kabewa ta markaɗa, idan kuma bata buƙatar markaɗa kabewar zata iya datsa ta ƙanana, idan an kawo markaɗen ta haɗe su wuri ɗaya. Sannan ta tafasa namanta haɗe da maggi da kuma spices, bayan ya tafasu, sai ta kwashe shi a wani kwano. Sannan ta zuba markaɗenta haɗe da mai ta soya, idan zata tsaida ruwan miya, sai ta haɗa da tafashen namanta, haɗe da ruwan jikinsa ta juye, sai ta ƙara ƴan ruwa, gwargwadon yadda take son yawan miyar.
Sai ta yanka alaiyyahu, ko Ugu, ko shuwaka, sai ta wanke su da gishiri saboda kashe ƙwarin da ke jikinsa, sai ta zuba a ruwan miyar, idan tana buƙatar egusi sai ta daka shi, ta haɗa maggi, da spices da albasa ta zuba a miyar.
Zata bashi ƴan mintuna kaɗan, da zaran miya ta yi, sai ta sauke.
Note: Miyar taushe mai kyau ana yin ta da kauri ne, idan ta yi ruwa tsururu, toh ba ta cika miyar taushe ba.