Yayin da tafiya ta kama mutum, kwana nawa kamata ya daina Sallar Ƙasaru a halin wannan tafiya?
Ana yin ƙasaru ne a tafiyar da ta kai tsawon Mil Arba’in da Takwas (48 Miles), matafiyi zai yi ƙasaru a kan hanyarsa ta tafiya, ko tsawon kwanaki nawa ne kafin ya isa inda yake da nufin zuwa. Sai dai idan matafiyin yana da niyar yin kwanaki Hudu (4), ko fiye da haka, kimanin kwatankwacin da zai yi Salloli 20. To, da zarar ya isa masaukinsa
Ƙasaru ta ƙare.
Amma in dai tafiyar ba ta kai kwana huɗu ba (Salloli 20), to, matafiyin zai iya ci gaba da ƙasarunsa har ya dawo garinsa.
A cikin Mazhaba ta Imamu Malik, ana yin ƙasaru ne a tafiyar da ta kai tsawon Mil Arba’in da Takwas (48 Miles) kawai. Kuma matafiyi zai ci gaba da ƙasarunsa matukar bai yi niyyar zama tsawon kwana hudu (4) ba, ko da kuwa ya wuce kwana huɗun, in dai tun alasi bai yi ƙudirin yin kwana huɗun ba.
A misali mutum ne ya yi tafiya don wata buƙatarsa, kuma ya ƙudiri cewa duk sanda ya samu abin da yake nema, to, washe gari zai dawo gida. To, irin wannan mutumin zai yi ta yin ƙasaru har tsawon kwanakin da ya yi yana jiran biyan buƙatarsa.
An samu wasu ƙalilan daga cikin magabatan da suke ganin cewa za a iya yin ƙasaru a tafiyar da ta kai mil 3, matuƙar dai a al’adance al’ummar tana ɗaukar irin wannan a matsayin tafiya. Sannan akwai wasu ‘yan ƙalilan da suke ganin cewa mutum zai iya yin ƙasaru tsawon kwana 10, ko 15 ko ma fiye. Amma fa wannan ra’ayi ne na ‘yan ƙalilan a cikin
magabata, wanda ya saɓa wa ra’ayin mafi yawan magabata. Kuma manyan malamai sun yi hani da ɗaukar irin wannan ra’ayin.
Ƙasaru da haɗa Sallah ga matafiyi a cikin tafiya abu ne shaharrare a gurin Malamai, kuma babu saɓani a wurin malamai, sannan yin hakan halal ne kuma sunnar Annabi (SAW) ne.
Amma fa idan matafiyi ya yi niyyar kwana huɗu, ko fiye da haka, Limaman mazhaba, kamar Imam Malik, Imam Shafi’i, da Imam Ahmad sun ce zai yi ƙasaru kuma ya haɗa Sallah a cikin tafiyarsa ne kawai, lallai ne ya cika sallarsa kuma ya yi ta a lokacin ta, da zarar ya isa masaukinsa (Wato ba zai yi ƙasaru ba kuma ba zai haɗa Sallah ba).
Wasu daga cikin magabata sun yi ƙasaru har tsawon wata shida, shekara ɗaya, kai har ma da shekara biyu.
Lallai masana sun tafi akan riƙo da abin da manyan Limamai suka tsaya a kansa, cewa bai dace musulmi ya yi ƙasaru ba idan ya yi niyyar kwana 5 a cikin tafiyarsa, kuma bai dace ya haɗa Sallah ba.
Sun bayyana cewa, abin da Annabi ya yi na yin ƙasaru a tsawon kwana 15 ko 19, don ana cikin yaƙin fatahu Makkah da Khaibar ne. Kuma sojojin da suke bakin daga, suna da wannan dama na yin ƙasaru da haɗa Sallah a bakin daga, komai tsawon lokacin da za su yi. Kuma abin da wasu magabata suka yi na yin ƙasaru tsawon wata shida, shekara ɗaya, ko
shekara biyu, kowanne na da dalilin yin hakan. Kenan yin haka a wajen mu bai dace da koyarwar magabata ba. Sai dai idan mutum ya samu kansa a cikin kwatan-kwacin halin da suka samu kansu a ciki.
Akwai ma’aikata da ‘yan makaranta masu yin ƙasaru da haɗa salloli, dogaro ga waɗancan hujjoji ya kamata su ji tsoron Allah su kyautata Ibadarsu ga Allah, kamar yadda mafi yawan magabata suka karantar. Kar ka bi ra’ayin ‘yan ƙalilan ka bar ra’ayin masu rinjaye, domin Sallah ba abar wasa ba ce. Don haka kar ka bari son sauƙi da arha ya tauye maka zinariyar Ibadarka ta Sallah.
Sai ka ga ma’aikaci ko dan makaranta yana yin ƙasaru da haɗa Sallah fiye da tsawon kwanakin da aka ƙayyade masa, bayan ya san cewa zai zauna a garin da yake aiki ko makarantarsu fiye da kwana huɗu. To, za ka iya yin ƙasaru da haɗa Sallah ne kawai a
lokacin da kake tsakiyar tafiya, da zarar ka isa masauki, to ƙasaru da haɗa Sallah sun kare.
Allah shi ne ma fi sani.