Waɗanne siffofi ne ake gane miji ko mace ta gari?
Mace Tagari da Miji Nagari:
Samun nagartaccen gida abu ne mai matukar muhimmanci a zamantakewar iyali. Shi kuwa gida ba ya zama nagartacce sai da mace tagari. Mace tagari kuma ita ce wadda take tattare da siffofi ababen koyi da za su taimaka mata wajen tafiyar da gidan yadda ya kamata. Akwai siffofi wadanda da an gan su a tattare da mace to kuwa ta kasance tagari ce. Siffofin sun hada da:
1. Mai kokarin neman yardar Ubangijinta. Ta hanyar sauke wajibabbun hakkokin da ke kanta.
2. Mai shiryar da mijinta (idan ya bata). Kuma tana taimaka masa wajen bin Allah da Manzonsa da Iyayensa da sadar da zumuncinsa.
3. Ba ta barin gidanta (don yaji, ko kuma yawon banza. Sai dai babban uzuri idan ya kama).
4. Ita ce mai tsananin kulawa da sallolinta biyar (Tana yin su a kan lokaci, kuma tare da tsoron Allah).
5. Ita ce mai boye sirrinta da sirrin mijinta (Ko sun bata da miji ko abokiyar zama, babu wanda zai sani).
6. Ba a ganin takalminta ko Kayan adonta idan tana tafiya (wato ta rufe jikinta baki daya).
7. Ba a jin sautin muryarta a ko’ina.
8. Ba a sanin kamannin siffar Jikinta (Ko yaushe tana sanye da tufafi kammalallu).
9. Abar girmamawa ce a cikin mutanenta, (saboda karamcinta da kyawun halayenta).
10. Mai kaskantar da kai ce a cikin zuciyarta. (Ba ta ganin cewa ita tafi karfin kowa)
11. Mai tausayi ce ga ‘ya’yanta, kuma tana kulawa da ciyar da su da shayar da su.
12. Gidanta tamkar wata Aljannah ce makusanciya (saboda soyayya da sakin fuska da wadatuwar Zuci).
13. Idan ta samu abin alkhairi daga maigidanta sai ta gode masa a fili da boye (Ko yaushe tana yi masa addu’a)
14. Idan ta riski wani sharri daga gare shi, takan yi hakuri. (Ba wai ta yi masa masifa ko haya-gaga ba).
15. Idan ya shigo gare ta sai ta yi farin ciki ta tare shi da murmushi. (Ba ta kullatar kowa a zuciyarta)
16. Idan ya fito daga gidanta (zai tafi wajen aiki) za ta nuna damuwarta, kuma tana dokin dawowarsa.
17. Idan yana fushi da ita takan yi hakuri ta jure, har sai ta ba shi hakuri ya huce.
18. Koyaushe idan ta matso gare shi sai ta burge shi (saboda kyawun ado da tsafta da kyawawan kalamai).
19. Idan ba ya nan, takan kiyaye masa amanar jikinta (ita kanta) da sirrinsa da gidansa, da dukiyarsa.
20. Idan ta ga wani laifinsa sai ta boye, ta suturce shi.
21. Idan ya gaya mata uzurinsa, takan karba ta yafe masa.
22. Mai tsananin Kunyar Allah ce da bayinsa. Hatta Maigidanta tana jin nauyinsa.
23. Mai gaskiya ce da rikon amana. (Bata yin karya don burge wani, ko kuma don tada husuma)
24. Mai girmama iyayen mijinta ce da danginsa. (Ba ta raina iyayen Miji, ko wulakanta ‘yan’uwansa).
25. Mai rufa asirin Mijinta ce yayin da talauci ya same shi (takan taimaka masa idan tana da iko).
26. Bata yi masa gori ko habaici ko cin fuska.
27. Ta runtse idanunta da zuciyarta. Ba ta kallon kowane namiji sai mijinta, kuma ba ta tunanin kowane namiji sai shi.
28. Tana kwantar da hankalin maigidanta duk lokacin da yake cikin wani yanayi. Ba ta zame masa baya. (Koda an bata masa rai a kasuwa ko a wajen aiki).
29. Tana nuna wa ‘ya’yanta yadda za su ga mutuncin mahaifinsu. Tana kula da tarbiyyarsu.
Bayan haka ta kasance mai riko da addini, ba mai sakaci da shi ba.
Ta kasance mai gaskiya da rikon amana a koyaushe.
Ta sanya Allah a ranta a duk al’amuranta na yau da kullum.
Ta kasance kwararriya wajen iya girki.
Ta kasance mai gaggawar amsa kira yayin da maigida ya kira ta zuwa shimfidarsa.
Ta kasance mai kiyaye dukiyarsa da duk wasu kayayyakin da yake amfani da su.
Ta kasance mai tausayi, ba mai jawo masa bukatun da ba zai iya biya mata ba.
Wannan ita ake kira mace tagari.
To amma dangane da miji nagari fa?
Miji nagari shi ne mutum mai ilimin addini, kuma wanda yake kwatanta aiki da iliminsa, wanda yake da dabi’u masu kyau. Lallai babu shakka wanda duk Allah Ya yi masa baiwar hada wadannan siffofi da dabi’u, Allah Ya yi masa babbar kyauta, kuma wannan shi ne ake kira miji nagari.
Miji nagari shi ne wanda ya hada wasu siffofi guda goma (10) wadanda Allah Ta’ala ya ambata a cikin sura ta 33 aya ta 35 inda Allah Ya ambaci maza da mata nagari. Kuma shi ne wanda manzon Allah SAW da kansa ya ce idan ya nemi mace da nufin aure to lallai a ba shi. Domin hana irin wadannan mazaje aure a lokacin da suka nema na iya sa iyayen yarinyar da ita kanta yarinyar su fada a cikin wata irin fitina da kuma barna a bayan kasa, haka dai fiyayyen halitta Annabin rahama SAW ya fada a cikin ma’anar hadisinsa ingantacce.
Abin lura a cikin wannan Magana ta manzon Allah SAW shi ne; mutum ba ya zama nagari saboda tarin iliminsa kawai amma babu dabi’a, haka kuma mutum ba ya zama nagari saboda kyawawan dabi’unsa kawai amma babu ilimi mai amfani. Wanda kawai yake zama nagari shi ne wanda ya hada wadannan abubuwa guda biyu, wato ilimin da ake aiki da shi da kuma kyawawan dabi’u.
Wata hanya ta biyu kuma na gane mutum nagari ita ce wajen alkhairinsa ga iyalansa da kuma yawan kyautata musu. A wani hadisi Manzon Allah SAW ya ce:
“Mafi alkaairinku shi ne mafi alkairi ga matansa, kuma ni ne mafi alkairinku ga iyalaina.” Don haka miji nagari shi ne mai kyautata wa matansa mai tausayinsu mai girmama iyayen matansa, shi ne kuma mai kulawa da hakkokinsu da Allah Ya dora a kansa gwargwadon ikonsa. Shi ne kuma mai yalwata kudin cefane da na kwalliya domin a samu abinci mai dadi kuma ta samu kudin gyara masa jikinta.
Miji nagari shi ne wanda yake yabawa da kwalliyar da matarsa ke yi masa, kuma yake yabon abincinta a duk lokacin da ya ci. Idan kuma an samu wani kuskure wajen dafa masa abincin, to yakan sanar da matarsa a cikin hikima da lafazi mai dadi.
Miji nagari shine mai kishin matarsa, domin manzon Allah SAW yace: Duk mutumin da ba ya kishin matarsa ba zai shiga aljanna ba. Miji nagari shi ne wanda yake son matarsa bayan ya aure ta fiye da yanda yake son ta kafin ya aure ta, shi ne wanda son matarsa ba ya fita a zuciyarsa har bayan mutuwarta. Domin manzon Allah SAW an kawo masa sarkar Nana Khadijah bayan rasuwar ta, yana ganin sarkar sai kawai aka ga hawaye na zubowa a fuskarsa, sai ya ce an tuna masa da matarsa Khadijah, saboda tsananin son da yake mata.
Wannan shi ake kira da miji nagari.
Wallahu Ta’ala a’alam.