NCC (Nigeria Communications Commission) da NITDA (National Information Technology Development Agency), wasu bangarori ne, wato agencies na Federal Ministry of Communication, Innovation and Digital Economy. An kirki NCC ne a shekarar 1992, ita kuma NITDA an samar da ita ne a 2001.
An kirkiri NCC ne kacokan don kula da duk wani abu da ya shafi sadarwa, wato telecommunications, a Nigeria, misali gidaje da kamfanonin telephone, radiyo da makamantansu. An kuma ƙirkiri NITDA don taimakawa wajen bincike, kirkire-kirkire da ba da shawarwari ga gwamnati ta yadda za ta samarwa ƙasa ci gaba ta hanyar IT, kamar su e-government, amfani da na’ura mai kwakwalwa a kowane sashe na rayuwa da ci gaba.
Nigerian Communication Commission (NCC)
Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC), ita ce hukumar kula da harkokin sadarwa ta kasa mai zaman kanta a Najeriya. Hukumar ita ce ke da alhakin samar da yanayin ayyukan sadarwa tsakanin kamfanonin da ke gudanar da sana’o’in tare da tabbatar da samar da ingantacciyar sadarwa a fadin ƙasa gabaɗaya.
A tsawon shekaru da NCC ta shafe, ta yi shura a matsayin babbar hukumar kula da harkokin sadarwa a Afirka ba ma a Najeriya kaɗai ba. Hukumar na da ƙudirin samar da damar amfani da na’urorin sadarwa na zamani don cigaban ƙasa ta fannoni daban-daban. Hukumar ta ɓullo da shirye-shirye da yawa don tallafa wa buƙatu da kuma bunƙasa kayan aikin ICT da ayyukan da suka dace.
Hakazalika don tabbatar da samun nasarar ayyukan hukumar, ta samar da tsarin bayar da lasisi da kuma ka’idojin da suka dace don samar da ayyukan sadarwa.
Dokar da ta kafa hukumar NCC
An kafa hukumar NCC a karkashin doka mai lamba 75 da gwamnatin mulkin soja, karkashin General Ibrahim Babangida, a ranar 24 ga watan Nuwamba 1992. An dorawa hukumar NCC alhakin kula da samar da ayyukan sadarwa da kayayyakin aiki, da ingantawa, da kuma ƙirƙirar ƙa’idojin gudanar da ayyukan sadarwa a Najeriya. An maye gurbin wannan doka da Dokar Sadarwa ta Najeriya (NCA) 2003.
Ikon hukumar NCC
Ikon Hukumar Sadarwa ta Najeriya ya samo asali ne daga sashe na 3 na Dokar Sadarwar Najeriya (NCA) na 2003.
- Ba da umarni a rubuce ga masu lasisi. Tuntuɓar masu amfani da na’urori, kamfanonin kasuwanci da masana’antu.
- Miƙa ayyukan hukumar ga kwamitin da ta kafa.
- Kiran mutane su bayyana a gaban Hukumar yayin da buƙatar hakan ta taso.
- Shigar da kwangila tare da kowane kamfani ko mutane.
- Kafawa da kuma kula da rassa don ba da damar sauƙaƙawa da rarraba ayyukan hukumar.
- Dangane da bayar da lasisi, an baiwa hukumar NCC iko da suka hada da:
- Tare da Bayar da lasisi da sanya sharuɗa a kan lasisi.
- Bambancewa ko soke sharadin lasisi. Tuntuɓar masu lasisin da abin ya shafa kafin fara aiki da wani wajibci wanda zai iya zama da wahala ga mai lasisi.
- Amincewa da tsarin ajiye kuɗi da tsarin ƙayyade farashin lasisi.
- Ba da izini ko soke izini don haɗin kayan aikin abokin ciniki.
- Ƙaddamar da ƙa’idoji don jagorantar shirye-shiryen haɗin gwiwa tsakanin masu aiki.
- Ƙaddamar da ayyuka da sababbin ayyuka da suka cancanci lasisi daga lokaci zuwa lokaci.
Ayyukan NCC
- Samar da saka hannun jari a ciki da shiga kasuwannin Najeriya don samar da ayyukan sadarwa da kayan aikin.
- Tabbatar da cewa masu lasisi suna aiwatar da aiki a kowane lokaci mafi inganci da kuma ingantaccen tsarin lissafin kuɗi.
- Bunƙasa yin gasa mai tsafta a tsakanin kamfanonin sadarwa da kariya daga sabis don samar da kyakkyawan aiki.
- Bayarwa da sabunta lasisin sadarwa daidai da tanade-tanaden doka da sa ido da aiwatar da bin ka’idojin lasisi da masu lasisi.
- Ba da shawara da aiwatar da gyare-gyare ga sharuɗan lasisi daidai da manufofi da tanadin doka.
- Kayyadewa da tattara kuɗaɗe don ba da lasisin sadarwa da sauran ayyukan da hukumar ke bayarwa.
- Ƙirƙirar da aiwatar da waɗannan ka’idoji waɗanda za su iya zama dole a ƙarƙashin wannan dokar don ba da cikakken ƙarfi da tasiri ga tanadin dokar.
- Gudanarwa da sarrafa mitar spectrum ta bangaren sadarwa da kuma taimaka wa Majalisar Kula da Mitar ta Kasa (NFM) wajen samar da tsarin mitar.
- Ba da shawara, ɗauka, bugawa da aiwatar da ƙayyadaddun fasaha da ƙa’idoji don shigo da kayan aiki da amfani da kayan sadarwa a Najeriya da haɗa kayan sadarwa cikin tsari.
- Ƙirƙirar da sarrafa abubuwan da Najeriya ke samarwa a cikin tsarin ƙa’idojin fasaha na duniya don ayyukan sadarwa da kayan aiki.
- Gudanar da gwaje-gwajen yarda da nau’in kan kayan sadarwa da bayar da takardun shaida bisa ƙayyadaddun fasaha da ƙa’idojin da hukumar ta tsara lokaci zuwa lokaci.
- Ƙarfafawa da haɓaka rabon ababen more rayuwa tsakanin masu lasisi da samar da ƙa’idoji a kansu.
- Bincike da warware korafe-korafe da ƙin yarda da aka shigar da kuma jayayya tsakanin masu aiki da lasisi, masu biyan kuɗi ko duk wani mutum da ke da hannu a cikin masana’antun sadarwa, ta amfani da irin waɗannan hanyoyin warware takaddama kamar yadda hukumar za ta iya tantancewa lokaci zuwa lokaci gami da sasantawa.
- Shirye-shirye da aiwatar da tsare-tsaren ingantawa da tabbatar da cigaban kamfanonin sadarwa da samar da ayyukan sadarwa a Najeriya.
- Ƙirƙira, sarrafawa da aiwatar da dabaru da shirye-shirye na Access Universal Access bisa ga manyan manufofin Gwamnatin Tarayya.
- Aiwatar da manufofin gwamnati na gabaɗaya game da kamfanonin sadarwa da aiwatar da duk wasu ayyuka da aka bai wa hukumar a ƙarƙashin wannan dokar.
- Wakilitar Najeriya a taron ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa da taron tattaunawa kan al’amuran da suka shafi ƙayyade hanyoyin sadarwa da sauran al’amura masu alaƙa da su.
Manufofin Hukumar NCC
- Don inganta aiwatar da manufofin sadarwa na ƙasa kamar yadda lokaci zuwa lokaci za a iya gyarawa.
- Don kafa tsarin masana’antar sadarwa ta Najeriya kuma samar da ingantacciyar hukuma, marar son kai kuma mai zaman kanta.
- Don inganta samar da ayyukan sadarwa na zamani, na duniya, mai inganci, abin dogaro, mai araha da sauƙi kuma mafi fa’ida a fadin Najeriya.
- Don ƙarfafa saka hannun jari na cikin gida da na waje a cikin kamfanonin sadarwar Najeriya da gabatar da sabbin ayyuka a kamfanonin daidai da mafi kyawun ayyuka na duniya.
- Don tabbatar da tsaftatacciyar gasa a dukkan kamfanonin sadarwa na Najeriya da kuma ƙarfafa gwiwar ‘yan Najeriya wajen mallaka da sarrafa kamfanonin sadarwa.
- Don kare haƙƙoƙi da muradan masu samar da sabis da masu amfani a cikin Najeriya.
- Don tabbatar da cewa an yi la’akari da buƙatun nakasassu da tsofaffi a tsarin samar da ayyukan sadarwa.
- Don tabbatar da ingantaccen tsarin gudanarwa wanda ya haɗa da tsarawa, daidaitawa, rarrabawa, ayyuka, rajista, saka idanu da amfani da ƙarancin albarkatun ƙasa a cikin sashin sadarwa.
National Information Technology Development Agency (NITDA)
Dokar Cigaban Fasahar Sadarwa ta Ƙasa ta shekarar (2007) ta ba da ikon ƙirƙirar tsarin bincike da bunƙasawa da daidaita aikace-aikace da saka idanu da tabbatar da ingancin ayyukan fasahar sadarwa mai kyakkyawan tsari a Najeriya.
Karkashin hakan ne aikin hukumar ya kasance bunƙasawa da tsarawa da ba da shawara kan fasahar sadarwa a cikin ƙasa, bisa ka’idoji da manufofi. Bugu da ƙari, NITDA ita ce cibiyar duk ayyukan IT da cigaban ababen more rayuwa a ƙasa. Ita ce babbar hukumar aiwatar da tsarin e-government da gudanar da harkokin intanet da cigaban fasahar IT gabaɗaya a Nijeriya.
Muhimman ayyukan NITDA
1. Software testing (Gwajin manhajoji)
Hukumar tana ƙoƙarin kawo ƙarshen ɗimbin asarar kuɗin da kamfanoni da kungiyoyi masu zaman kansu ke yi wajen sayan manhajoji, ta hanyar samar da ɗakin gwaje-gwaje don tabbatar da inganci da zai bai wa masu saye damar tantancewa a lokacin da ake sayan kayayyakin. Manufar ita ce ƙarfafa aiwatarwa da tura manhajoji na asali domin su zama karɓaɓɓu masu kyau don biyan buƙatun masu amfani.
Na daga cikin ayyukan hukumar ƙarfafawa da haɓaka ingantattun manhajoji na cikin gida don cigaban tattalin arziki mai ɗorewa.
Har ila yau hukumar ta himmatu domin raba Najeriya da gurɓatattun manhajoji marasa inganci, tare da inganta ayyukan masana’antun sarrafa manhajoji
2. ICT clearance (Tabbatar da fasahar ICT)
Hukumar NITDA a matsayinta na jigo a fagen ayyukan IT a Najeriya, an wajaba mata kula da tabbatar da dukkan ayyukan IT daidai da manufofin gwamnatin tarayya, don ƙara nuna gaskiya da rikon amana wajen gudanar da ayyuka a cibiyoyin gwamnati.
Saboda haka ne ma, Gwamnatin Tarayya ta fitar da wata doka mai lamba SGF/6/S.19/T/65 a ranar 18 ga watan Afrilu, 2006, inda ta umurci duk cibiyoyin gwamnati da ke shirin fara duk wani aikin IT, da su nemi izini daga NITDA.
3. Registration of service providers (Rijistar kamfanonin sadarwa)
Hukumar NITDA ita ce ke ba da izinin samar da ka’idoji don fasahar (IT) da bunƙasa ƙwarewar gida a bangaren ICT ga Najeriya. Don haka, bisa ga wannan umarni, hukumar ke yin rajistar kamfanonin sadarwa da ke samar da sabis na fasahar sadarwa (IT) masu ba da kwangila ga ma’aikatu da sassan hukumomin (MDAs) na Gwamnatin Tarayya.
Manufar rajistar shi ne don tabbatar da isar da ayyuka masu inganci da ɗorewa ga gwamnati, don zurfafa ƙwarewa a ayyukan IT da kuma tabbatar da cigaban ingantattun kamfanonin IT na asali a Najeriya.
4. Domain registration (Rijistar adireshin yanar gizo)
Wannan tsari ne don yin rijistar domain (wato adireshin yanar gizo). Duk gidajen yanar gizo/shafuka a kowane mataki walau Tarayya, Jihohi da Kananan Hukumomi ko ayyuka na musamman na gwamnati waɗanda za su ɗauki tsawon watanni 18 ko sama da haka ana buƙatar yin rajista a ɓangaren .GOV.NG da .MIL.NG.
Akwai hanyoyi guda biyu don yin rajistar sunan domain GOV.NG ko MIL.NG. Ana iya aikawa da rubutacciyar buƙatar hakan zuwa hukumar (NITDA) ko kafar rijista ta Intanet
Kammalawa
Hukumomin guda biyu dukkansu suna aiki ne a kan harkokin sadarwa, buri da manufar kowace shi ne samar da ingantaccen tsarin mai tafiya da zamani a fannin fasahar sadarwa. A cikin maƙalar an yi bayani daki-daki ta yadda zai gamsar da mai buƙatar sanin bambancin ayyuka tsakanin hukumar NCC da kuma ta NITDA ta Najeriya.