A harkokin cryptocurrency da ke ci gaba da bunƙasa a wannan zamani, zaɓar ingantacciyar manhajar musayar kuɗaɗen da cinikayyarsu abu ne mai mauhimmanci domin haɓaka riba da kauce wa haɗari da kuma asara. Bitget, Binance da Bybit su ne manyan manhajoji guda uku a kasuwar crypto, kowannensu na da fa’idoji na musamman. Wannan maƙala ta shiga cikin duniyar crypto ta farauto wa masu karatu da manazarta gamsassun bayanai game da wadannan manhajoji don taimakawa wajen yanke shawarar wace manhaja ce ta fi dacewa da buƙatun kasuwancinku.
Mene ne cryptocurrency?
Cryptocurrency wani fagen kasuwancin kuɗaɗe ne na tsarin dijital (na zamani) inda mutane ke iya saya, sayarwa, ko kasuwancin cryptocurrencies (wato kuɗaɗen yanar gizo). Wannan fage kamar cinikayyar hannun jari ne inda mutane ke gudanar harkokin kasuwancin wani kamfani ko masana’anta. Sai dai a nan, ana hulɗa da kuɗaɗen dijital ne kamar Bitcoin, Ethereum, da sauransu.
Ta ya ya cryptocurrency ke aiki?
Akwai matakai da yawa da ake bi kafin mutun ya tsinci kansa cikin wannan kasuwar hada-hadar kuɗaɗe, waɗannan matakai sun hada da:
Yin rijista
Shi wannan fage na kasuwancin kuɗaɗen crypto yana farawa da yin rajista da ɗaya daga cikin manhajojin da ke gudanar da harkar cryptocurrency, kamar dai yadda ake ƙirƙirar asusu a shafin yanar gizo.
Mallakar wallet
Da zarar an yi rijista, nan take mutun zai samu wallet ɗin dijital a cikin manhajar, wannan wallet yana aiki a matsayin jakar ajiya amma a tsarin dijital. Wato a cikinsa ne ake adana su kuɗaɗen cryptocurrencies ɗin.
Saye da sayarwa
Mutane na iya amfani da kuɗaɗensu na yau da kullun, kamar Naira ko Daloli ko Yuro don sayan cryptocurrencies. Wannan shi ne sashen da ake musayar kuɗi na ainihin da kuɗin dijital. Haka nan za a iya sayar da kuɗin digital don musayar kuɗaɗen yau da kullun lokacin da ake buƙata.
Damar musaya
Kamar musanya Naira da Dalar lokacin da mutum zai yi tafiya zuwa nahiyar Turai ko kuma Afrika, ana iya musayar cryptocurrency daga wani zuwa wani.
Samar da tsaro
Manhajoji masu nagarta suna ɗaukar tsaro da mahimmanci. Suna amfani da fasahohin tsare sirri da sauran hanyoyin don kiyaye jakar wallet ɗin abokan hulɗarsu.
Ƙayyade farashi
Farashin wannan kuɗaɗe na iya canjawa koyaushe, kamar yadda kasuwar hannun jari ke yi. Don haka, mutane sukan saka idanu a kan farashi da yin ciniki lokacin da suka ga farashin ya yi kyau.
Bayanin manhajojin guda uku: Bitget, Binance da Bybit
1. Bitget
An kirkiro manhajar musaya da sayar da kuɗaɗen crypto ta Bitget a cikin shekarar 2018, Bitget ita ce babbar manhajar musanyar cryptocurrency da kamfanin Web3 ya samar. Tana ba da damar yin aikace-aikace ga masu amfani da ita har sama da miliyan 100 a cikin ƙasashe da yankuna fiye da 150. Bitget ta himmatu wajen taimaka wa masu amfani da ita su yi kasuwanci tare da inganci da sauran hanyoyin kasuwancin kuɗaɗen dijital na zamani, har ma da damar samun farashin kuɗaɗe irin su Bitcoin, Ethereum, da sauran nau’ikan kuɗaɗe. A da ana kiran wannan manhajar da suna BitKeep, Bitget Wallet, wallet ce ta duniya gabaɗaya wacce ke ba da ɗimbin ingantattun hanyoyin sarrafa Web3 da abubuwa kamar ayyukan wallet, musanya, NFT da sauran su.
Su waye suka kirkiro Bitget?
Bitget ta shiga cikin fasahar blockchain a cikin shekarar 2015 lokacin da rukunin masu ƙirƙirar manhajar suka zama masu sha’awar harkar hada-hadar crypto bayan nazarin bunƙasar kuɗin Bitcoin da kuma hasashe game da Ethereum. An kaddamar da Bitget a hukumance a cikin shekarar 2018. Tun daga lokacin manhajar take haɓaka sosai.
Bayan haka, Bitget ta zama wata cibiyar masu hangen nesa na farko game da blockchain, karkashin jagorancin babbar jami’a – Gracy Chen, sai babban jami’in ayyuka – Vugar Usi Zade, da babban jami’in kasuwanci – Min Lin, da kuma babban jami’in shari’a – Hon NG.
Ƙasashen da babu Bitget
Bitget tana da abokan ciniki a ƙasashe da yankuna sama da 100 a duniya, yayin da ta hana ko keɓe wasu ƙasashe da yankuna daga cikin da’irar fasaharta, wanda suka haɗa da: Amurka, Singapore, Koriya ta Arewa, Sudan, da sauransu.
Kuɗaɗen ake a hada-hadarsu a Bitget
Bitget tana ta’ammali da ɗimbin kuɗaɗe masu yawa sama da guda 800 da suke cikin tsarin crypto, tana da nau’ikan hada-hadar kasuwanci sama da 900. Shahararrun kuɗaɗen a wannan manhaja sun haɗa da BTC, ETH, BGB, XRP, PEPE, DOGE, SHIB, BNB, LTC, APT da sauran su.
2. Binance
Binance, wacce aka samar a cikin shekarar 2017, ta samu karɓuwa da sauri inda ta zama ɗaya daga cikin manyan manhajojin musanyar cryptocurrency a duniya. Tana da hedikwata a Hong Kong kuma ta shahara saboda yawan abubuwa da kayan aikin cryptocurrencies da suka mayar da ita mai matuƙar amfani, da tsauraran matakan tsaro. Yawaitar hada-hadar yau da kullun ta Binance tana cikin mafi muhimmancin abubuwa a cikin manhajar, wannan ya mayar da ita manhajar da mutane suka fi so.
Su waye suka kirkiro Binance?
Changpeng Zhao da Yi He ne suka samar manhajar tare da kafa mata hedikwata ta duniya a kasar Sin. CZ mutum ne mai gina shafukan yanar gizo da manhajoji, kuma mai kula da harkokin kasuwanci, shi ne shugaban kamfanin. Ya yi karatu a jami’ar McGill Montreal kuma yana da kyakkyawan tarihi a matsayin ɗan kasuwa. Mukaman da ya riƙe a baya sun haɗa da shugaban kamfanin Bloomberg Tradebook Futures Research & Development team, shi ne ya kafa kamfanin Fusion Systems da kuma zama shugaban sashen fasaha na Blockchain.com.
Yi He shi ne CMO a Binance kuma Shugaban a Binance Labs, babban mai hannun jarin kamfanin. Yi, a baya mataimakin shugaba ne a kamfanin mobile video tech company, Yixia Technology, ya kuma ba da gudunmawa wajen kafa manhajar musayar kuɗaɗe ta OKCoin.
Ƙasashen da babu Binance
A ƙarƙashin sharuɗɗan amfani na manhajar Binance, ƙayyadaddun wuraren da aka daƙile fasahar sun haɗa da Amurka, Singapore da Ontario (Kanada). Haka nan wasu ƙasashe sun iyakance amfani da ita ko wasu abubuwan a cikinta saboda dalilai na tsaro, amma ba a iyakance su ga, China, Malaysia, Japan, UK da Thailand ba. A cikin Satumba 2019, an ƙaddamar da wata kebatacciyar manhaja ta musamman don abokan cinikinta na ƙasar Amurka, wannan manhaja ana kiran ta Binance.US.
3. Bybit
Bybit ita ce manhajar musayar cryptocurrency ta biyu mafi girma a duniya ta fuskar hada-hada, tana hidimta wa ga al’ummar duniya masu amfani da ita sama da miliyan 60. An ƙirƙiro ta a cikin shekarar 2018. Shahararriya ce ta fuskar tsaro da inganci a fagen cinikayya da musanyar kuɗaɗen crypto daban-daban tare da wadatattun kayan aikin fasahar blockchain na zamani. Bybit tana bunƙasa tare da cike giɓi tsakanin TradFi da DeFi, ƙarfafa wa masu zuba jari, masu ƙirƙira, da masu sha’awar kutsawa cikin duniyar fasahar Web3.
Su waye suka kirkiro Bybit?
Wanda ya samar kuma ya shugabanta shi ne Ben Zhou. Bayan ya kammala karatunsa daga Jami’ar Pennsylvania, Zhou ya koma kasar Sin kuma ya yi aiki na tsawon shekaru 7 a kamfanin XM, ɗaya daga cikin manyan kamfanonin dillalai a kasar Sin. A cikin shekarar 2018, ya ƙirƙiro crypto Bybit. Kamfanin yana da rijista a tsibirin Virgin Islands a matsayin Bybit Fintech Limited, kuma yana da hedikwata a Dubai, UAE, karkashin Bybit Fintech FZE.
Ƙasashen da babu Bybit
Wannan manhaja tana samuwa ga mutane a duk faɗin duniya, ban da ƙasashen da aka dakatar da fasahar manhajar kamar Amurka, United Kingdom, China, Hong Kong, Singapore, Canada, Koriya ta Arewa, Cuba, Iran, Uzbekistan, yankunan da Rasha ke da iko da shi na Ukraine (a halin yanzu ciki har da Crimea, Donetsk, da Luhansk), Siriya.
Kuɗaɗen ake a hada-hada a Bybit
Bybit tana hada-hadar kuɗaɗen crypto sama da 100 da aka jera a cikin manhajar, tare da nau’ikan hada-hadar kasuwanci sama da 300, manyan daga cikin kuɗaɗen su ne: BTC, ETH, BIT, SOL, Biri, DYDX, LT, DOGE, AVAX, MATIC, DOT da sauran su.
Adadin kuɗaɗen da manhajojin suke caja: Bitget, Binance da Bybit
Ɗaya daga cikin muhimman abubuwan da ke da alaƙa da zaɓar manhajar musayar crypto shi ne kuɗaɗen da kowacce manhaja ke caja idan mutum ya saya ko ya musanya.
• Bitget
Bitget tana cirar mafi ƙarancin kuɗin caji, musamman ga saye da sayarwa marasa yawa. Don haka yayin ciniki ƙalilan, ana cajin masu fitarwa da masu karɓar kashi 0.20%, tare da ragin kashi 0.14% idan aka yi amfani da kuɗaɗen Bitget mai alamar (BFT) don biyan kuɗin ciniki. Cajin cirar kuɗi ya dogara ne a kan yawan kuɗaɗen, an tsara shi a 0.05%.
• Binance
Binance na da ɗabi’ar gasa wajen cajin mutane kuɗi yayin amfani da manhajar, mai fitarwa da mai karɓa ana canjin su kashi 0.1%. Bugu da ƙari, Binance tana ba da rangwame ga masu amfani da ita waɗanda ke biyan kuɗi ta amfani da nau’in kuɗi mallakar manhajar, wato BNB. Wannan ya sa Binance ta zama zaɓi mai ban sha’awa ga ‘yan kasuwa a kodayaushe.
• Bybit
Bybit, tana ci gaba sosai da bunƙasa ta hanyar ba da damar musayar cryptocurrency kyauta idan ba shi da yawa. Wannan babbar fa’ida ce ga ‘yan kasuwa waɗanda ke juya ƙananun kuɗaɗe. Haka kuma, cajin da Bybit kan yi shi ma matsakaici ne, yayin da ake cajar mai fitarwa 0.01% mai karɓa kuma 0.06%.
Gabaɗayansu, Bitget, Binance da Bybit suna ba da kayayyaki da aikace-aikace da yawa, wanda suka haɗa da shahararrun kuɗaɗen cryptocurrencies kamar Bitcoin (BTC), Ethereum (ETH), da Ripple (XRP). Binance tana alfahari da hada-hadar kuɗaɗen crypto sama da 460, wannan ya mayar da ita manhaja mai kunshe da nau’ikan kuɗaɗe daban-daban don ‘yan kasuwa da ke neman saka hannun jari a harkar cryptocurrencies daban-daban. Bybit, yayin da take ba da ƙananan nau’ikan kuɗaɗen crypto sama da (320), ta yi fice a wannan fage na kasuwancin crypto.
Idan ana magana game amfani, dukkan manhajojin suna ba da damar yin amfani da hasashen 1: 100 game da farashi a lokaci na gaba. Wannan babban alfanu na iya zama takobi mai baki biyu, wato yana ba da damar samun riba mai yawa, amma kuma yana ƙara haɗarin hasara mai yawa. Ya kamata ‘yan kasuwa su tunkari cinikin da aka yi amfani da hasashe cikin taka-tsan-tsan tare da tabbatar da cewa suna da ingantattun dabarun sarrafa asara.
Tsaro da ƙa’idoji
Tsaro shi ne babban abin damuwa a cikin duniyar crypto, kuma dukkan manhajojin, Bitget, Binance da Bybit suna ɗaukar shi da mahimmanci. Bitget tana jaddada tsaro ta hanyar amfani da sa hannu masu yawa tare da taimakon fasahar A+ SSL, tana inganta kayan aikin tsaro.
Binance tana ɗaukar matakan tsaro da yawa, wanda suka haɗa da fasahar tsaro ta (2FA), jerin saƙon cirewa, da lambobin anti-phishing. Koyaya, Binance ta fuskanci kutse na tsaro a cikin ƙasashe daban-daban, wanda zai iya haifar da damuwa ga wasu masu amfani da ita.
Haka nan Bybit tana aiwatar da ƙarfafan ƙa’idojin tsaro, wanda ya ƙunshi tsarin 2FA da SSL. Kamar Binance, Bybit ba ta da kulawar kowace hukumar kuɗi a matakin farko, wanda hakan zai iya zama koma baya ga ‘yan kasuwa waɗanda ke ba da fifikon a kan tsaro.
Damar samun kuɗin shiga
Bitget, Binance da Bybit suna ba da dama ga ‘yan kasuwa don samun kuɗin shiga na yau da kullun. Bitget tana ba da damar yin aikace-aikace don taimaka wa masu amfani da ita samun kuɗin shiga cikin sauƙi. A nan akwai wasu shahararrun hanyoyin samun ƙarin kuɗi a cikin manhajar Bitget. Binance tana samar da aikace-aikacen crypto kamar mining da yawa, yana ba wa masu amfani damar samun lada a kan abin da suka mallaka. Bybit ma tana da fa’ida a wannan babi, amma ta bambanta kanta tare da ƙarin damarmaki kamar hakar mining ɗin DeFi da zuba hannun jari.
Wace manhaja ce ta fi?
Tabbatar da wace manhaja ce ta fi tsakanin Bitget, Binance da Bybit ya dogara da buƙatun kasuwancin mutun da abubuwan da yake so.
Bitget Token (BGB) yana ba masu amfani keɓantaccen alfanu da haƙƙoƙi, kamar rangwamen caji, samun dama ga manyan kuɗaɗe ta hanyar manhajar Launchpad, zaɓi cikin jerin ayyukan manhajar, da sauran su. Bitget na da tsabar kuɗin mai alamar BGB har biliyan 1.4 da ke gudana tare da jimullar biliyan 2 a asusu.
Bitget tana tabbatar wa abokan hulɗarta ƙwarewa da gogewa a fagen hada-hadar crypto. Binance tana da kyau ga ‘yan kasuwa waɗanda ke neman nau’ikan cryptocurrencies, ingantacciyar manhajar musayar kuɗaɗen crypto da sauran ayyuka kamar NFTs da ETFs.
Bybit, a gefe guda, ta fi dacewa ga ƙwararrun ‘yan kasuwa da suka mayar da hankali kan kasuwancin abubuwa masu daraja, sarrafa ƙananan kuɗaɗe, da sabbin damarmakin samun kuɗin shiga.
Idan aka ba da fifiko ga kadarori da kuɗaɗen musaya daban-daban da kuma samun manhaja mai kyau da inganci, Binance na iya zama mafi inganci. Idan ana bukatar manhaja da za a riƙa amfani da ƙananan kuɗaɗen kasuwanci da ta ƙunshi abubuwa na musamman don kasuwancin crypto, Bybit na iya zama zaɓi mafi muhimmanci. Dukkansu suna da fa’idojinsu da rauninsu, don haka mafi kyawun zaɓi zai dogara ne a kan takamaiman manufar kasuwanci da burin da ake da shi.
Manazarta
CoinMarketCap. (n.d.). Binance trade volume and market listings | CoinMarketCap
CoinRanking. (n.d.). BitGet: Exchange Ranking & trading Volume. Coinranking
CryptoSlate. (2022, July 27). Bybit | CryptoSlate
What is Cryptocurrency and How Does it Work? (2018, December 8)