Ko da na shiga sallah an tsere mini da wasu raka’oi. Bayan liman ya sallame, sai na tashi zan cika abinda ya tsere mini. Ina cikin hakan sai wasiwasi ya kama ni, misali ina kokwanton shin raka’o’i biyu suka tsere min, ko uku, ko ma daya. Na kasa daidaito akan guda. To amma a gefena akwai wani mamu da na tabbata a lokaci guda muka shiga sallar da shi.
Shin zan iya la’akari da shi na cika sallata, ko kuwa me ya kamata na yi a wannan yanayi?
Lawan Dalha Edited question August 30, 2024