Shin shan taba sigari da cin goro yana da illa ga lafiyar mutane? Idan yana da ita mece ce illar?
Goro nau’in abin ci ne wanda hausawa suke girmamawa, musamman a cikin bukukuwan aure da kuma suna. Sannan har ila yau hausawa kan yi kyautar girmamawa da shi, kuma suke kallon shi a wata alama ta albishir a tattare da shi.
Sai dai kuma duk da wannan matsayi na sa, ba kowa ne ke cin sa ba, sai tsofaffi, ko masu ciki, ko kuma masu shan taba sigari, duk da akwai mutanen da suke cin sa, kuma ba tsofaffi ne ba.
Sai dai wasu mutane kan soki cin goro saboda yadda yake canja kalar haƙora zuwa launin ja. Daga baya ma wasu da yawa na ganin cin goro na da matuƙar illa ga lafiyar mai ci. A wani bangaren kuma an gano amfanin da goro yake shi kamar haka:
Amfani 10 da Goro ke yi a jikin Dan Adam, Wasu likitoci sun yi kokarin wayar da kawunan mutane game da amfani da macen goro ta ke da shi a jikin dan Adam. Likitoci da suka yi bincike kan amfanin goro sun bayyana cewa ɗaya daga cikin amfanin da goro yake yi ya haɗa da gyara huhun mai shan taba sigari.
1. Magance ciwon kai musamman wanda ake kira da ‘Migrain headache.
2. Goro na maganin lalurar zawo.
3. Tana tafiyar da gajiya.
4. Goro na rage kiba musamman ga wadanda suke fama da ita.
5. Tana taimaka wa mutanen da suke fama da kasala saboda tana duke sa sinadarin ‘Caffen’.
6. Tana hana yin amai.
7. Tana kawar da jiri.
8. Goro na maganin ciwon dajin ‘ya’yan marainan namiji.
9. Yana maganin mura da cutukan da ya shafi makogoro da hanci.
10. Yana hana kamuwa da cutuka Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu.
Kaɗan daga cikin illar da goro yake yi kuwa shi ne: yana sanya warin baki, sannan ya kan chanja haƙora zuwa launin ja.
Sannan idan ya kama mutum ya zama addicted, da wahala ya iya bari, a ƙa’ida kuma komai ana son yin amfani da shi yadda ya dace, domin kare lafiya daga kamuwa da cutuka.
Shan taba sigari ba abu ne mai kyau ba ga lafiyar Ɗan adam, domin illar farko da take da ita shi ne “Masu shan taba suna yawan mutuwa da ƙuruciyarsu”, kamar yadda masu kamfanin tabar suka faɗa da kansu, kuma mutuwa da ƙuruciya ba abu ne da kowa ke so ba, sai wanda Allah ya ƙaddara mawa.
A Addinance kuwa shan taba na cikin nau’in almubazzaranci, domin babu wani amfani da take da shi a jikin Ɗan’adam, sai dai asarar kuɗaɗe, shi kuma almubazzaranci haramun ne a musulunci, domin Allah Maɗaukakin Sarki ya ce “Kada ku yi almubazzaranci, domin masu yin almubazzaranci ƴan uwan shaiɗan ne, shi kuma shaiɗan ya kafirce ma Ubangijinsa.”
Wata uwa da take yi ma ɗanta nasiha ta ce “Shan taba sigari daidai yake da ka ɗauki kuɗinka ka cinna musu wuta”, ta cigaba da cewa “Kai gwara ma ka cinna ma kuɗinka wuta zai fi, domin hakan ba zai cutar maka da lafiya ba, saɓanin shan taba sigari da ke haifar da cutuka masu illah.”
Don haka shan taba sigari a Addinance haramun ne, domin daidai take da almubazzaranci, sannan jefa kai a halaka ne, kuma Allah Maɗaukakin Sarki ya ce “Ka da ku jefa kanku a halaka.”
A lafiyance kuwa shan taba sigari na kawo kansar hunhu (Lung cancer), tana haifar da tarin tibi (Tuberculosis), sannan tana kawo warin baki, da ma Cancer ta baki, wani likitan musulunci ya ce “Matan da mazansu ke shan taba wuya suke sha, musamman a wurin shimfiɗa, saboda bakinsu wari yake.”
Daga ƙarshe kuma tana kawo lalacewar fata, domin mai shan taba jikinsa ya kan yi baƙi, ta yadda da an gansa ake ganewa.
Don haka babu wani alfanu a shan taba sigari, sai ma muguwar illar da take da ita. Da fatan Allah ya tsare mu Amiiiiin.