Me ya sa ƴan mata da zawarawa suka fantsama sosai a shiga harkar Film?
Shin neman kuɗi ne? Ko kuma shahara ce suke nema??
Neman kuɗi da neman shahara abubuwa ne mabambanta, sai dai suna tafiya kafaɗa da juna. Don haka idan muka duba za mu ga cewa; akwai ‘yammata ko zawarawa da suke shiga harkar fim saboda neman kuɗi, Akwai kuma waɗanda suke shiga saboda neman shahara.
Idan muka yi duba ga waɗanda suke shiga domin neman kuɗi za mu ga cewa yawancinsu talakawa ne, ko kuma masu neman sana’ar da za ta dinga kawo musu kuɗi, don haka idan talauci ya dame su sukan shiga harkar fim domin su samu kuɗin da za su rufa wa kansu asiri, sau da yawa ma sukan fito daga gidan mazajensu ne idan suka rasa hanyar ɓullewa sai su fada harkar fim, idan ya kasance da gaske neman kuɗin suka fito sai su mayar da hankali a kan sana’ar domin su samu kuɗin, tun da da yawa idan an yi hira da su suna faɗin sun ɗauki harkar fim sana’a shi ya sa suka shigo.
Akwai kuma waɗanda suke shiga harkar fim ɗin domin shahara ba domin neman kuɗi ba, su kuma waɗannan yawancinsu suna da kuɗin da ma, kuɗin fim babu abin da zai kare su da shi, shi ya sa suke shiga domin neman shahara a san fuskokinsu.
Sai dai kuma akwai waɗanda talakawan ne amma ba su damu da samun kuɗin ba a fim sai shahara, su dai kawai a san fuskokinsu su shahara sosai ko da ba za su samu kuɗi ba, sannan kuma akwai waɗanda ba su damu da shaharar ba, su dai kawai su samu kuɗi ko da ba su shahara ba. Akwai kuma waɗanda duka suna yin fim ne don shahara da neman kuɗi, suna so su samu duka abubuwan guda biyu.
Kenan dai kowa da manufar da take kawo shi cikin biyun nan, ko dai neman kuɗi ko kuma shahara.
Allah Ya sa mu dace.