Mabiya addinin kirista sun yi imani cewa Yesu Almasihu (Annabi Isah) ɗan Allah ne, yayin da Musulmai suka aminta da cewa shi Annabin Allah ne kawai. Kawo dalili na yarda ko rashin yarda game da wannan batu tare da hujjoji masu ƙarfi.
Yesu Almasihu(Annabi isa A.S) ba Allah bane,hujja.
Sunan mahaifiyarsa Maryam Imrana. Mahaifiyarta Hannatu, mahaifinta yana cikin manyan mutane a cikin jama’ar Banu-isra’ila har ma shi ne yake limanci a masallacin Qudus.
Yayinda matar Imrana ta sami cikinsa ta rika fatan abin da za ta haifa ya zama namiji har ma ta yi bakance idan ta haifi namiji zai zama hadimin masallaci, amma da ta tashi haihuwa sai Allah ya ba ta ‘ya mace. Hannatu babar Maryam ta damu qwarai saboda bakancen da ta yi, amma duk da haka sai ta yi wa Allah godiya kuma ta ambace ta da suna Maryam, Ma’anarsa shi ne, WANDA BATA DA AIBI.
Iyayen Maryam sun rasu tana qarama saboda haka sai Annabi zakariya ya dauke ta ya cigaba da renonta, har ma ya gina mata ɗaki na musamman a cikin Masallaci. Babu wanda yake shiga dakin sai shi. Nana Maryam tun tasowarta ba ta da wani aiki sai ibada dare da rana. Duk sanda Annabi Zakariyya ya kawo mata ziyara sai ya tarar da abinci da kayan marmari a wajenta, idan ya tambayeta wa ya kawo mata wannan sai ta ce: Daga Allah ne, domin Allah yana arzuta wanda ya so, ba tare da hisabi ba.
kamar yadda tarihi ya nuna cewa nanne gurin da aka haifa Annabi Isah Alaihissalam.
Yayin da kuma Nana Maryam ta kai munzalin girma sai al’ada ta zo mata, saboda haka, sai ta fita bayan gari wajen wata qorama don ta yi tsarki, sai Mala’ika Jibril ya zo mata a siffar wani saurayi daga Banu Isra’ila mai suna Taqiyyu, shi wannan mutum ya yi qaurin suna da ɓarna a wannan lokaci Allah Madaukakin Sarki ya ce, “Sai muka aika mata da ruhu (shi ne mala’ika jibrilu) ya je mata a surar saurayi, sai ta ce “Ni ina neman tsari da Ubangijin Rahama daga gareka idan kai ne Taqiyyu. “Sai Mala’ika Jibril ya ce, mata “Ni Manzon Ubangijinki ne, Allah ne ya aiko ni. Domin in ba ki kyautar ɗa mai qwazo.
“Sai ta ce da shi: Ta ya ya zan sami ɗa, bayan wani mutum bai shafe ni ba, kuma ni ban taɓa yin alfasha ba? Sai ya ce: Haka al’amarin yake, haka Allah Ya hukunta, kuma wannan abu ne mai sauqi a wajen Allah. Allah ya ce: “Za mu sanya shi ya zama izina a wajen mutane, kuma Rahama daga garemu, wannan lamari ne zartacce.” (Surar Maryam, Aya ta 17) Mala’ika Jibrilu yana gama wannan bayanin sai ya kama gefen rigarta ya yi busa a ciki, nan take sai Allah ya halicci Annabi Isah a cikin cikinta. Malam wahabu ya ce: Tsakanin ɗaukar cikin Annabi Isah da haifarsa sa’a guda ne kawai, saboda faɗin Allah Ta’ala ya ce, “Sai ta ɗauki cikinsa, sai ta tafi da shi wuri mai nisa, sai naquda ta zo mata a wajen kututturen dabino, sai ta ce: Ya kaicona dama na mutu kafin faruwar wanan na zama mantacciya abar mantawa.”
Sai Allah ya ce; Sai muka kirata ta qarqashinta muka ce: Kada ki yi baqin ciki, Allah ya gudano da qoramar ruwa a kusa da ke, ki girgiza kututturen dabinon nan zai zubo miki da lubiya nunanniya, ki ci, ki sha, ki kwantar da hankalinki. An ce wannan dabinon da ta girgiza shekararsa saba’in bai yi ‘ya’ya ba, amma ana haihuwar Annabi Isah a kusa da shi, nan take sai ya yi ganyen, ya fitar da ‘ya’ya saboda mu’ujizar Annabi Isah (A.S.)
An ruwaito cewa; Yayinda Maryam ta je wajen mutanenta tana ɗauke da Annabi Isah (A.S.) sai suka ce; Ya ke Maryam lallai kin zo da babban lamari, ya ‘yar’uwar Haruna mahaifinki ba mutumin banza ba ne, mahaifiyarki ma ba mutuniyar banza ba ce. Yayinda ta ji wannan zargi daga mutanenta sai ta yi musu nuni da Annabi Isah tana nufin su tambaye shi. Sai suka ce: Ta ya ya za mu yi magana da jariri a cikin zanin goyo?
Sai Allah ya buɗi bakin Annabi Isah ya ce da su:
“Ni bawan Allah ne ya bani littafi yasan yani Manzo yayi albarka a gareni duk inda nake yayimin wasiyya da sallah da Zakka matukar ina raye, sannan da yin biyayya ga Mahaifiyata. Bai san yani shakiyyi mai girman kai ba, farkon Kalmar da Annabi Isah ya fara magana da ita itace, ni bawan Allah ne domin yanke hanzari ga wadanda za suce shi dan Allah ne.
Kamar yadda ya zo a cikin qur’ani,a cikin suratul Maryam
Juz 16 / Hizb 31 – Page 307
Annabi isa da kansa ya ce,
إِنِّى عَبْدُ ٱللَّهِ ءَاتَىٰنِىَ ٱلْكِتَـٰبَ وَجَعَلَنِى نَبِيًّۭا ٣٠
Annabi isa ya ce, “Hakika ni bawan Allah ne. Ya ƙaddara a ba ni Littafi, in zama Annabi.
وَجَعَلَنِى مُبَارَكًا أَيْنَ مَا كُنتُ وَأَوْصَـٰنِى بِٱلصَّلَوٰةِ وَٱلزَّكَوٰةِ مَا دُمْتُ حَيًّۭا ٣١
kuma ya umurce ni da in tsai da salla, kuma in bayar da zakka matuqar ina da rai.
وَبَرًّۢا بِوَٰلِدَتِى وَلَمْ يَجْعَلْنِى جَبَّارًۭا شَقِيًّۭا ٣٢
da kuma kyautatawa mahaifiyata. Bai sanya ni mai girman kai ko mai taurin kai ba.
وَٱلسَّلَـٰمُ عَلَىَّ يَوْمَ وُلِدتُّ وَيَوْمَ أَمُوتُ وَيَوْمَ أُبْعَثُ حَيًّۭا ٣٣
Amincin Allah ya tabbata a gare ni ranar da aka haife ni, da ranar da zan mutu, da ranar da ake tayar da ni.”
Anruwaito cewea yayin da Annabi Isah ya girma sai yarika yawo aba yan kasa, baya zama da waje daya, saboda haka ma bai taba mallakar dakin kwana ba. Bare gida ko mata, ko abun hawa tufafinsa kuma jubbace ta sufi. Baya cin abinci sai daga kasabin Mahaifiyarsa ta kasance tana saka tufafi tasiyar suci abinci. a irin wayace-wayacen da yake yi ya je wani gari da ake cewa Nasira a qasar Sham, shida mahaifiyarsa suka zauna a can.
Saboda haka ne ake dan ganta mutanensa da sunan wannan garin ake ce musu NASARA.
Haka kuma Ka’abur Akabari ya ce; Yayin da addinin Annabi isah ya yazo ya cika ko’ina, mutane suka yi ta shiga addinin daga ko’ina, sai addinin Yahudanci ya yi rauni, Allah ya saukarwa Annabi Isah Littafin Linjila, ya zama yana raya matattu da ikon Allah, yayin da wani sarki mai suna Hardusa ya ga haka sai ya yi nufin zai kashe Annabi Isah (A.S.) ya sami goyon bayan wasu daga manyan malaman Yahudawa. Sai suka shirya suka kai masa hari a lokacin yana tare da mahaifiyarsa suka wakilta wani daga cikinsu don ya shiga ɗakin ya kashe shi. Kafin ya shiga sai Allah ya ɗauke Annabi zuwa sama, ya shiga yanan ta dube-dube bai gan shi ba, sauran waɗanda suke waje da suka ga ya daɗe bai fito ba sai suka bi shi suna shiga sai suka ga ɗan uwansu, Allah ya sa masa kamannin Annabi Isah komai da komai, sai suka kama shi suka ɗaure suka sa masa hular gashi, suka kewaye gari da shi, sannan suka kafa azarori guda biyu suka gicciye shi a kanta, suka kashe ɗan uwansu, suna zaton Annabi Isah suka kashe.
Allah Madaukakin Sarki ya ce; “Ba su kashe shi ba, ba su gicciye shi ba, sai dai cewa Allah ya ɗuakaka shi ya zuwa gare shi. An ruwaito cewa: A lokacin da suka kashe ɗan uwansu ya kasnace ranar Juma’a ne da misalin ƙarfe uku na rana, sai duniyad ta yi duhu, tsawon kwanaki uku, a kai girgizar qasa a wanan rana.
Malam Sa’alabi ya ruwaito cewa: Lokacin da aka ɗauke Annabi Isah zuwa sama shekarunsa talatin da biyar a duniya. Sai Allah Ta’ala ya sara masa zabi’a irin ta Mala’iku ya zama baya buqatar ci da sha, kuma har yau yana nan a raye kamar yadda Hadisai ingantattu suka tabbatar.
Malam Sa’alabi ya qara da cewa: nana Maryam Allah ya qara mata yarda ta yi wafati bayan ɗauke Annabi Isah da shekara shida. An ce ta rayu tsawon shekara sittin. Kabarinta a yanzu haka yana masallacin qudus ana ziyararsa.
Saboda haka Annabi Isa ba Allah bane,ba kuma ɗan Allah bane, Annabin Allah ne.
Madalla da wannan jawabi naki.