Na ji wani masani ya bayar da tabbacin cikin wa ita kalmar ‘so’ ɗin ma ba Bahaushiyar kalma ba ce, wannan ne ya haskaka cewa kalmar ‘ƙauna’ ita ake da ita a Hausa.
Bahaushe na amfani da kalmar so ne a yayin da yake nufin ƙauna. Ke nan a tunanin Hausawa ƙauna da so abu ɗaya ne.
Sai dai wani hanzari ba gudu ba: masanin da ya bayyana kalmar so a matsayin a rarriyar kalma ya yi bayanin cewa an samo kalmar ne daga harshen Berber (Tuareg), wanda su a wajensu wani abu daban take nufi amma yana da alaƙa da abin da muke nufi da so.
A yanzu mu dawo da hankalimu game da ma’anar kalmomin biyu: – idan jin wani baƙon yanayi na musamman mai ɗauke da bege ko shauƙi a kan wani mutum ko wani abu shi ne ƙauna, so shi ma haka Bahaushe yake nufi da shi. Idan haka ne, to babu bambanci.
Masu son bambantawa suna kafa hujja da cewa ƙauna ita ce mataki na gaba da so, ma’ana wani mataki masoyi ke kaiwa a so sai ya risƙi ƙauna… Amma idan aka san tushe da asalin kalmomin za a gane cewa babu bambanci. Hasali ma a wajen Balarabe babu sama da so (alhub), domin ƙauna (ishq) ɗaya ce daga cikin ire-iren so.
Madalla. Sannu da ƙoƙari.