Kawo taƙaitaccen tarihin marigayi Jafar Adam.
TAƘAITACCEN TARIHIN MARIGAYI SHEIK JA’AFAR MAHMUD ADAM KANO.
An haifi marigayi Sheikh Ja’afar Mahmoud Adam ne a garin Daura, a farkon shekarun 1960s. Marigayi Ja’afar ya fara karatunsa na allo a gidansu a Daura, a wurin mijin yayarsa, Malam Haruna, wanda kuma dan’uwansu ne na jini. Daga nan kuma sai aka mayar da shi wajen wani Malam Umaru a wani gari “Koza” da ke Arewa da Daura a jihar Katsina.
Bayan sun zo Kano ne tare da wannan malami a 1971 sai ya zauna a makarantar Malam Abdullahi a cikin Fagge. Da ma can Sheikh Ja’afar ya riga ya fara haddar Alkur’ani maigirma, wanda ya kammala a shekara ta 1978. Bayan da Malamin ya haddace Alkur’ani ne sai ya ga bukatar ya samu ilmin Boko don haka ya fara karatun zamani a 1980.
Har wa yau, Malam Ja’afar ya shiga makarantar koyon Larabci ta mutanen kasar Misra a cibiyar yada al’adun kasar Misra (Egyptian Cultural Centre), sannan kuma ya shiga makarantar Boko ta manya watau “Adult Evening Classes.” A 1983 ne Malamin ya kammala wadannan makarantu 2 na Boko da Arabiyya, wanda daga nan ya samu shiga makarantar GATC Gwale a 1984, har ya kammala a1988. Bayan shekara guda ne ya wuce Jami’ar Musulunci ta Madina. A wannan babbar jami’ar musulunci ta Madinah ne Malamin ya karanta ilimin tafsiri da Ulumul Kur’an, wanda kuma ya kammala a shekara ta 1993. A wancan lokaci ne aka soma jin tafsirin sa na Al-Qur’ani a cikin Garin Maiduguri. Bayan nan Sheikh Ja’afar ya samu damar kammala karatunsa na digiri na biyu (Masters) a Jami’ar Musulunci ta Oundurman a kasar Sudan. Kafin rasuwar Malamin, ya yi nisa wajen karatunsa na PhD) a Jami’ar Usman Danfodio ta Sokoto.
Kamar yadda Malamin ya fada daga cikin malamansa na ilimin addinin Musulunci, akwai malaminsa na farko, mutumin kasar Masar, Sheikh Abdul-Aziz Ali al-Mustafa, da kuma Malam Nuhu a unguwar Dandago da ke cikin Kano. A wajen Malam Dandago ne Marigayin ya karanci ilimin fikihun malikiyya da wadansu littattafai na hadisi. Sauran Malaman sun hada da Muhammad Shehu, mutumin Lokoja, wanda Malam ya karanci nahawu da sarfu da balaga da adab. Akwai kuma Sheikh Abubakar Jibrin limamin masallacin Juma’a na BUK, akwai kuma Dr. Ahmad Muhammad Ibrahim shi ma na jami’ar Bayero ta Kano. Daga cikin malamansa na jami’a kuma, akwai Sheikh Abdurrafi’u da Dr. Khalid Assabt da sauran su.
Haka nan; daga cikin karatuttukan da Malam Ja’afar Adam ya gabatar, ya sauke Al-Qur’ani kusan sau 2 a Masallacin Muhammad Indimi da ke cikin Garin Maiduguri a jihar Borno, a cikin shekaru barkatai. Malam ya kuma karantar da Kitabuttauhiid na Sheikh Muhammad Ibn Abdulwahab, da kuma littatafan hadisai na Umdatul Ahkaam, Arba’una Hadiith. Sauran darusa sun hada da wani littafin tauhidi da ya fice mai suna Kashfusshubuhaat. Haka kuma Malam ya karantar da litaffin nan na Bulugul Maraam, Riyaadussalihiin, Siiratun Nabawiy, da kuma Ahkaamul Janaa’iz, Siffatus Salaatun Nabiiy na Muhammad NasirudDeen Albany.
Wasu daga cikin daliban malam sun hada da Malam Rabi’u Umar R/Lemo da Malam Sani Abdullahi Alhamidi Dorayi da Malam Abdullah Usman Gadon Kaya da Malam Usman Sani Haruna da kuma Malam Ibrahim Abdullahi Sani. Sauran manyan Almajiran Marigayin sun hada da Malam Ali Yunus Muhammad da Dr. Salisu Shehu da Malam Shehu Hamisu Kura da kuma Malam Anas Muhammad Madabo. Kafin rasuwarsa, Malam ya fara gagarumin aikin rubuce tafsirinsa a harshen Hausa a karkashin wannan cibiya (Sheikh Ja’afar Islamic Documentation Centre).
Marigayi Sheikh Ja’afar Mahmoud Adam ya rasu ranar Juma’a 26/Rabii’u Awwal/1428 (daidai da 13/04/2007). Malamin ya rasu ya bar mata biyu, da ‘yaya shida, yayin da aka haifa masa ta bakwai kwanaki 58 daidai bayan an yi masa kisan gilla. Dubun-dubatar mutane ne daga ko’ina cikin kasar nan suka halarci jana’izarsa, kuma an binne shi ne a makabartar Dorayi. Allah ya ji kan sa ya gafarta masa, ya saka masa da gidan Aljannatul-firdausi, ameen.
Ma Sha Allah. Sannu da ƙoƙari.