Ya matsayin shan taba Cigarette 🚬 a Musulunci?
Sannan wace irin illah take da ita ga lafiyar ɗan adam?
MATSAYIN SHAN TABA A MUSULUNCI:
Ubangiji yakan haramta abu ne a gare mu saboda dalilin cutarwar da wannan abun yake da shi a gare mu. Ko dai cutarwa ta fuskar hankali ko lafiya ko zamantakewar al’umma.
Irin su giya da wiwi da ƙwayoyi da duk wasu abubuwa masu sanya maye, Allah Ya haramta mana su ne saboda cutarwar da suke sanyawa ta fuskar hankali. Sun cutar da hankalin masu mu’amala da su, tun da suna juyar musu da hankali su fidda su daga hayyacinsu.
To ita ma Taba Sigari (Cigarettes) tana cikin wannan ajin ne. Ba ta da wani amfani ko kaɗan. Kuma Tana cutar da lafiyar masu shan ta. Ko da kamfanonin da ke yin ta sun tabbatar da haka. Shi ya sa ma suke rubutawa a jikin ta.
Sayen taba Sigari almubazzaranci ne. Kuma Allah Maɗaukaki ya ce.
“HAKIKA SU ALMUBAZZARAI SUN ZAMANTO ‘YAN UWAN SHAITAN NE. SHI KUWA SHAITAN YA ZAMANTO MAI KAFIRCEWA NE GA UBANGIJINSA.”
To idan ka yi nazari da idon basira, za ka ga cewa ashe kenan babu wanda zai sha taba sigari face sai wanda bai damu da lafiyar jikinsa ko zubewar mutuncinsa ba.
ILLOLIN SHAN TABA SIGARI:
Shan taba sigari na daga cikin babbar matsalar da ta fi lashe rayukan masu shan ta.
Kuma a cikin duk masu shan taba biyu, ɗaya daga cikinsu kan mutu ne sakamakon larurorin da shan tabar ke jefa su.
Shan taba sigari na da gagarumar illa ga dukkanin jiki kamar haka:
Zagayawar jini: Kamar yadda aka sani ne cewa zagayawar jini shi ne zagayawar rayuwa.
Sai dai yayin da gubar da ke ɗauke cikin hayakin taba sigari ya shiga cikin jini hakan zai sa:
a) Kaurin jini ya ƙaru, wannan zai ƙara haɗarin daskarewar jini.
b) Ƙaruwar wahalar hauhawar jini da ingiza bugawar zuciya fiye da ƙima; wannan zai ƙara wa zuciya wahalar harba jini zuwa sassan jiki.
c) Cunkushewar ko matsewar hanyoyin jini; wannan zai rage wa sassan jiki samun isashshen jini.
Huhu wanda a nan ne ake canjin iska tsakanin iskar “oxygen” da muke shaƙa da iskar “carbondioxide” da muke fitarwa waje.
Shan taba sigari na rage wannan aiki baya ga lalata tanadin kariya da Allah ya shirya wa huhun, wannan zai karya garkuwar huhun ta yadda cututtukan numfashi kamar tarin Tibi, sankarar ko dajin huhu za su kama mutum cikin sauƙi.
Waɗannan illoli na shafar dukkan sauran sassan jiki kamar zuciya, jijiyoyin jini, kayan ciki, fata, ƙashi da raguwar ƙwayoyin halittar haihuwa da dai sauransu.
A taƙaice dai bayan dumbum illolin shan taba sigari, dukkanin wata cuta ko larura shan taba sigari na ta’azzara ta.
Shan taba na iya yin mummunar illa ga jikin mutum. Shan taba yana ƙara haɗarin cutar kansar huhu, da kuma sauran nau’ikan kansar kamar su mafitsara, pancreatic, da ciwon makogwaro.
Haka nan, shan taba yana iya ƙara haɗarin cututtukan zuciya, hawan jini, da bugun jini. Yana iya lalata aikin fahimi, kamar ƙwaƙwalwar ajiya da iya yin yanke shawara, ƙara haɗarin haɗari da rauni, kuma haifar da baƙin ciki da damuwa.
Shan taba na iya haifar da mummunar illa ga jikin mutum, gami da:
Ƙara haɗarin kansar huhu, da sauran nau’in ciwon daji kamar su mafitsara, pancreatic, da ciwon makogwaro.
Cutar sankara na yau da kullum da emphysema, wanda zai iya haifar da wahalar numfashi da tari na yau da kullun.
Ƙara haɗarin cututtukan zuciya, bugun jini, da hawan jini.
Rage aikin huhu da ikon motsa jiki.
Ƙara haɗarin cutar danko da asarar hakori.
Tsufa da wuri da murɗawar fata.
Rage aikin tsarin rigakafi, yana sauƙaƙa rashin lafiya.
Wadannan munanan illolin na iya haifar da su ta hanyar sinadarai masu cutarwa da yawa da ke cikin hayakin sigari, gami da kwalta, carbon monoxide, da sauran gubobi. Idan mutum ya dade yana shan taba da kuma yawan sigari da yake shan taba kowace rana, zai fi girma haɗarin kamuwa da manyan matsalolin lafiya. Sabili da haka, yana da mahimmanci a daina shan taba ko kuma a taɓa fara shan taba tun da farko don rage haɗarin waɗannan sakamakon rashin lafiya.
Nazarin da aka yi a kan sama da mutane dubu 50,000, ya nuna cewar sauyin da ake samu a jerin kwayoyin halittar dan adam yana taimaka wa ayyukan da huhu yake yi, kuma yana rage tasirin da shan taba yake yi.
Majalisar masana kimiyya ta ce abubuwan da aka gano a nazarin zai iya samar da sababbin magunguna da za su kara lafiyar huhu.
Amma kuma a cewar masana kimiyyar, ba lallai ba ne shan sigari ya zamanto zabi mafi kyau.
Masana kimiyyar sun kara da cewar mafi yawancin masu shan taba, za su kamu da ciwon huhu.
Amma kuma wadanda ba su taba shan tabar ba ma a rayuwarsu, suma za su iya kamuwa da ciwon huhun.
Waɗannan kaɗan ne daga cikin illolin shan taba sigari.
WALLAHU TA’ALA A’ALAM.