Dangane da halaccin bin sallar gawa ga mata, babu inda aka haramta wa mata halartar sallar janazah (wato sallar gawa) suna da damar yin ta domin su ma su riski falalar da ke cikin ta. Manzon Allah ﷺ ya ce.
“Duk wanda ya halarci sallar gawa har aka sallace ta, to yana da Qeerati guda. Wanda kuwa ya halarce ta har aka binne ta to yana da Qeerati biyu na lada.”
Sai aka ce, “Ya Rasulallahi mene ne Qeerati biyu?”
Sai ya ce, “Kamar misalin girman manyan duwatsu guda biyu.”
(Bukhariy da Muslim da Abu Dawud da Ahmad ne suka ruwaito shi).
To kenen a cikin wannan falalar ba a keɓance maza kaɗai ba, wato har da mata kenan.
Ko da rakiyar gawa ma, idan suka je za su samu lada kamar yadda maza za su samu. Hujjar farko wannan hadisin da ya gabata. Hujjah ta biyu kuma hadisin Ummu ‘
Atiyyah wanda take cewa:
“An hana mu bin janazah (wato rakiyar gawa) amma ba a tsananta hanawar gare mu ba.”
Bukhariy ya ruwaito shi akan lamba ta 1278. Muslim ma ya ruwaito shi a cikin Kitabul Jana’iz hadisi mai lamba 34 da 35.
Imam Muhammad bin Isma’il As-San’aniy a cikin sharhin da ya yi wa wannan hadisin sai ya ce, “Cewar da ta yi “Ba a tsananta hanin gare mu ba” hujjah ce a zahiri cewa hani ne bisa karhanci ba wai haramci ba.”
A gaba kaɗan ya ƙara da cewa, “Dukkan malamai ma’abota ilimi sun tafi a kan cewa wannan hanin na karhanci ne, ba haramci ba.”
Kuma hujjar da ke ƙara ƙarfafar haka shi ne hadisin da Ibnu Abi Shaibah ya fitar ta hanyar Abu Hurairah (Allah ya yarda da shi) cewa.
Watarana Manzon Allah ﷺ yana wajen wata sallar janazah sai Sayyidina Umar ya ga wata mata har ya yi mata tsawa. Sai Manzon Allah ﷺ ya ce, “ƘYALE TA YA UMARU.”
Imamun Nisa’iy da Ibnu Maajah ma sun fitar da hadisin ta hanyoyi ingantattu.
Don ƙarin bayani a duba Subulus salam sharhin Bulugul Maram juzu’i na 2 shafi na 555.
Kuma waɗannan hadisan ba su ci karo da hadisin Abdullahi ɗan Abbas ba, wanda a cikinsa ya ce.
“Manzon Allah ﷺ ya tsine wa mata masu yawan ziyartar ƙaburbura da masu rikon ƙaburbura a matsayin wuraren masallatai da wuraren kunna fitilu.”
Tirmidhiy da Nisa’iy da Abu Dawud da Imamu Ahmad ne suka ruwaito shi.
Shaikh Ahmad bin Yahya Annajmiy a cikin littafinsa mai suna TA’ASEESUL AHKAM (Juzu’i na 3 shafi na 134) da ya zo yin sharhi a kan wannan hadisin tsinuwar, cewa ya yi:
“Wannan ana nufin matan da ke tafiya zuwa maƙabartu domin yin ziyara irin ta bidi’ah ko ta shirka.” (Wato masu yawaita ziyara da niyyar aikata haramtattun abubuwa a shari’a).
A takaice dai ya halatta mata su halarci sallar janazah, kuma ya halatta su je maƙabarta domin halartar binne wani makusancin su, ko kuma domin su ziyarci ƙabarin wani su yi masa addu’a.
Dr Muhammad Bakr Isma’eel a cikin littafinsa mai suna FIQHUL WADHIHU juzu’i na ɗaya shafi na 409 ya ware babi na musamman wanda a cikinsa ya faɗi hukuncin halartar mata wajen sallatar mamaci.
Ya ce, “Halartar sallar janazah ya halatta ga mata, bisa sharaɗin za su kasance cikin cikakkiyar sutura, ba tare da bayyanar da ado ba, ba tare da sun fitini kowa ba, ba tare da sun shafa turare ba.
Domin haƙiƙa Tabaraniy ya ruwaito hadisi a cikin Mu’ujamul Kabeer tare da kyakkyawan isnadi cewa Sayyidina Umar bin Khattab ya tsimanyi matarsa Ummu Abdillah har sai da ta sallaci ‘Utbah (wani ɗan’uwanta ne).
Sai dai ya fi kyau gare su idan sun halarci wajen sallar, su tsaya a bayan mazaje. (wato kada su tsaya a wajen da maza za su gan su).
Imamu Muslim ya rawaito hadisi.
A’isha Allah Ya ƙara mata yarda lokacin da Sa’ad ɗan abin waƙas ya rasu, matayen Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama sun umarci a kawo musu gawarsa su yi masa Sallah. Aka kawo musu shi suka yi masa.
Wannan ya nuna mata suna Sallah ga gawa, ko dai su yi a gida kafin a fitar da gawar, ko kuma su yi tare da maza a waje, amma sahunsu ya zama yana baya.
Dangane da zuwan mata domin ziyartar ƙabari kuwa, mutukar dai sun kiyaye sharuɗan da aka faɗa a sama, to ya halatta su je. Domin kuwa Imamu Malik da Imam Abu Hanifah da Imamu Ahmad bin Hanbal duk suna ganin halaccin shi. Saboda dalilai da hujjoji da dama.
Misali kamar hadisin Ibnu Abi Mulaikah a lokacin da ya ga Nana A’isha ta fito daga maƙabarta ta ziyarci ɗan’uwanta Abdurrahman bin Abibakrin, sai ya ce mata.
“Shin ba Manzon Allah ﷺ ya hana ziyartar ƙabari ba?”
Sai ta ce masa.
“Eh da farko ya hana ziyartar ƙabari, amma daga baya ya yi umurni a dinga ziyarta.”
Hakim da Baihaqiy ne suka ruwaito shi kuma Imam Zahabiy ya ce ingantacce ne.
Sannan akwai hadisin Anas bin Malik (Allah ya yarda da shi) wanda Bukhariy da Muslim suka ruwaito, cewa, Manzon Allah ﷺ ya ga wata mace tana kuka a kusa da wani ƙabari sai ya ce mata, “Ki ji tsoron Allah ki yi haƙuri.”
Ya wuce ya tafi, bai hana ta ziyarar ba, ihun da take yi ya hana.
WALLAHU A’ALAM.