Waɗanne abubuwa mutum zai tanada idan zai yi noman Tumatur? Kuma yaya ake yin noman Tumatur din?
Shuka tumatir aiki ne mai sauƙi wanda za a iya yi a cikin lambun gida, bayan gida, ko ma a cikin kwantena a baranda. Ga jagorar mataki-mataki kan yadda ake shuka tumatir:
Kafin a fara aikin noma, yana da muhimmanci a samu ƙasa mai kyau. Wannan ƙasa ba kowacce iri ake amfani da ita ba, dole ne ta kasance tana ɗauke da sinadarai waɗanda zasu taimaka wajen girma da ci gaban shuka.
Matakai na Hada Kasan Noman gida –
Akwai waɗanda ke nesa da gona ko kuma ba su da sauƙin samun ƙasa mai kyau, wanda hakan ke kashe musu karsashin noman cikin gida. Amma, wannan ba dalili bane. Idan kuna sha’awar koyon yadda ake hada ƙasa domin noma cikin sauƙi, ga matakan da za ku bi:
1. Samun Kasar Bola:
Idan inda kuke akwai ƙasar bola, wannan zai fi kyau. Idan kuka samo ƙasar bola, ku cire duk wani datti ko duwatsu da ke cikin ƙasar. Wannan ƙasar tana da sinadarai masu amfani ga shuka, kuma tana taimaka wa shuka wajen girma da kyau. Zaku iya amfani da wannan ƙasar domin yin noma.
Akwai cuttutuka sama da arbain da biyar da suke kama tumatur wanda kwari sama da ashirin suke samarwa.
Amma kafin jin yadda ake maganinsu da kuma kaman ce-ce niyar su ga yadda ake noman tumatur din a buhu ko gida ko kango ko lambu.
Da farko zaka nemi iri domin akwai iri kala biyu akwai determine da kuma indeterminate Variety, banbancin su kawai shine shi determine yakan iya ɗurar ruwa ajikin sa wato moisture wadda ƙarancin ruwan zai yi wuya yayi masa illa.
Za kuma ka gyara inda zaka fara rainon wannan irin. Zaka zuba takin compound fertiliser wato mai ɗauke da npk 15:15:15. Ka guji zuba takin gida saboda kaucewa ƙwarin cikin ƙasa da kuma cuttutukan da kashin dabbobin suke ɗauke da shi.
Zaka baza takin da yakai 5kg a filin da zakw raini irinka mai tsayin meter ashirin da faɗin meter goma. Zaka ringa yin ramin saka iri mai tsayin centimetres goma da kuma barin ta zarar centimetres goma tsakanin ramin daka saka iri a baya ko na gefe ko kuma na gaba.
Da zarar ka gama saka irin zaka rufe shi da ƙasa ka kuma yayyafamasa ruwa. Sai kuma ka nemo bushashiyar ciyawa ka rufe wajen da ita.
Bayan kwana biyar zuwa takwas zaka ga irin ka ya fara fita. Sai ka fara ɗibar irin naka da zuwa dasawa a gona ko kuma lambu ko kuma buhu.
Ba,a dasa irin da bai kai tsayin centimetres goma ba! Ko kuma wanda yafi wannan girma, Ko kuma wanda tun yana ƙaramin sa ya fara flowering.
Da zarar anje inda za,a dasa shi idan ana gujin ko akwai ƙwarin cikin ƙasa za,a saka sinadarin maganin ƙwari na nemagon a filin wajen. Idan anzo ɗebo irin za,a dasa sa ana ɗauko shi da ƙasar dake jikin jijiyarsa.
Ana yin dashen tumatur ne da sanyin safiya ko kuma da yammaci lokacin rana ta faɗi. Sannan kuma ana zuba masa takin urea wato nitrogen mai yawan 250kg a duk hectre ɗaya kafin a dasa shi wanda ke cika buhu biyar kenan.
Da zarar ya kama ƙasa bayan sati uku ana ƙara masa wani takin sannan kuma idan da damuna ne ya banbanta da lokacin rani wajen zuba masa ruwa!
Idan kuma ƙasar wajen mai taɓo ce ko kuma mai rike ruwa ce. ban ruwa sau daya a sati ma ya isa. Idan kuma kasar wajen bata riƙe ruwa sosai ban ruwa sau biyu a sati ya isa!
Ana fara cire masa ciyawa tun daga kwana ashirin da biyar zuwa talatin da shida. Wato sati huɗu da yin dasansa. Saboda a lokacin ciyawa take damunsa. Ko dai ka sa hannun ko kuma kasa maganin kashe ciyawa.
Sannan akwai cututtukan tumatur sama da guda arbain da biyar wanda kwari ashirin suke samarwa.
To cututtukan da suka fi kamar guda biyar ne. Akwai leafblight da kuma early blight wanda duk cuttutukan fungi ne.
Sannan kuma akwai bacterial disease da kuma waɗan su da ake maganin su.
Da farko ka nemi iri mai juriya da kuma yin feshi akai-akai dama zuba musu ruwa gudun kada karancin ruwa ya saka suyi yawa.
Idan za kayi feshi kayi da 0.5kg metachlor da kuma metribuzim da kuma 5kg na sulphuric acid. Wanda wannan maganin laraforce da kuma zforce za suyi maka.
Zaka fara cire tumatur ɗin na farkon girbi tun daga ranar 44 zuwa hamsin da biyar.