Waɗanne irin alamomi ne mutum zai gane masoyinsa na son rabuwa da shi?
HANYOYIN DA MUTUM ZAI GANE MASOYINSA YANA SON RABUWA DA SHI.
Mafi yawan matan da suke son rabuwa da samarinsu suna gudun duk wani abin da ya fito daga gare su, komai tsananin son da suke yi wa abin muddin ya fito ne daga wajen saurayin da suke son rabuwa da shi,to ba za su taba yarda su karbi wannan abin ba, ko da kuwa kuɗi ne ko wata kyauta ta musamman da saurayin zai ba wa yarinyar bayan gama zance ba za ta taba karba ba, wata ma a wajen za ta bar duk abin ba tare da ta taba ba, sai dai a gida a gani a dauka.
Macen da take son rabuwa da saurayinta ba za ta taba son a yi zancensa ba, ko da kuwa wani labari ne da ya shafe shi ba za ta so ji ba, idan kana son ganin damuwarta ka yi mata zancen shi.
Haka kuma mace na jinkirta fita har na tsahon lokuta a duk sa’in da aka sanar mata ya zo wajen ta zance, ko kuma ta fara barcin Karya, ba don komai ba sai don ya gaji ya tafi.
Idan kuwa aka tilasta mata har ta fita yana tare da bacin rai domin za ta zama tamkar bebiya mara magana ne, don duk abin da zai ce ba za ta taba tanka masa ba, idan kuwa ta tanka to iya ciki ne, ba tare da ya ji me ta ce masa ba, haka zai ta babatu shi kadai.
Wani ma in bai ci sa’a ba ko sallama ba za a yi masa ba a yayin da ta iso, haka kuma za ta rufe fuska da mayafi ko kuma ta kalli wani gefen can daban, gudun ka da ma ya kalli fuskar.
Batun kwalliya kuwa ta haramta wa kanta yi don ba za a taba yi masa ba, sai dai idan da ma da kwalliyar ya zo ya same ta, wata ma ko da a ce da kwalliyar a fuskarta ya zo, to zuwa za ta yi ta wanke, ita lallai ba za ta bayyana masa wani kyanta ba, ko don ya daina son ta tun da tana son rabuwa da shi ne.
Batun kiran waya kuwa ba za ta kira shi ba, kuma ko da ya kira ta ba za ta taba yarda ta daga wayar ba, muddin kuwa ta daga take za ta canja murya cikin salo mara dadin saurare wata ma har ta kara bude murya tamkar muryar namiji, wata tana yi tana sauri-sauri kamar ana jiran ta, wata kuma tana yi tana daukar mintuna kafin saukar amsar da yake son ji daga gare ta.
Wata kuma za ta bawa wani yaron ko wata yarinyar ta daga ne da zummar ba ta nan, ko tana sallah ko tana barci ko makamancin hakan.
AKwai alamomi da dama waɗanda mata ke nuna wa namiji muddin suna son rabuwa da namijin da yake son su.
Idan kana so ka gane mace tana son rabuwa da kai ba ta son ka, na farko za ka ga sau da dama idan kana mata magana sai dai ka ji tana eh, umm, Na biyu kuma kallon raini a fakaice, ko ta dinga hararar ka, na uku in ka tura a kira ta ba ta fitowa da wuri sai ta ga dama ta fito, na hudu, ba ta fiya yin Kwalliya ba in ka zo ko a yaya take za ta fito, na biyar ba ta damuwa da ta kira ka ko da kuwa ‘please call me’ ko ‘flashing’ ne, na shida ba ta son ana ma ta zancen ka ko da da wasa ne.
In ka ba ta kyauta ba ta farin ciki bare ma ta yi maka godiya, in ka nemi zuwa gidansu kuwa duk yadda za ka yi ba za ta taba yarda ba.
Dangane da yadda samari suke son rabuwa da ‘yammatansu kuwa, akwai alamomi da suke nuna wa da yawa, amma ga kaɗan daga ciki:
Idan kika ga namiji ba ya kula da al-amuranki yadda ya kamata to akwai wadda yake so, kuma yana son rabuwa da ke ne.
Idan kika ga namiji ba ya zuwa wajen ki zance akai-akai to ki gane yana son rabuwa da ke ne ƙila ya samu wata.
Idan kika ga namiji kin ce masa ya je ya gaida iyayenki yana yi miki hanya-hanya to tun wuri ki gane ba don ki yake yi ba hanyar rabuwa da ke yake nema.
Idan kika ga namiji ba ya sakar miki fuska yadda ya kamata to akwai matsala ba kya gabansa ne rabuwa zai yi da ke.
Idan kika ga namiji yana yi miki labarin wata
can daban to ba ke ce a ransa ba, hanyar rabuwa da ke yake nema.
Idan kika ga namiji ba ya yi miki faɗa a kan rashin daidai da kika aikata to ki bi a sannu rabuwa da ke zai yi.
Idan kika ga namiji yana yawan hantarar ki a kan abun da bai kai ya kawo ba to fa sai a hankali yana son rabuwa da ke ne.
Idan kika ga namiji ba ya son ɗaga wayarki kuma shi ba ya kiran ki sosai to da walakin goro a miya. Tabbas yana son rabuwa da ke ne.
Waɗannan hanyoyi ne kaɗan daga cikin hanyoyin da mutum zai gane masoyinsa yana son rabuwa da shi.