Sanin kowa ne, ciwon sanyi wato (Infection/ Toilet Infection) ya zama gagara badau wurin addabar Al’ummah, har ta kai ga wasu ma’aurata suna samun saɓani a zamantakewarsu ta dalilin wannan ciwo. Toh ta ya mutum zai iya kare kansa daga kamuwa da wannan cuta? Sannan idan ya kamu, wace hanya ce zai bi wurin magance wannan cuta?
Yadda za a ƙare kai daga kamuwa da ciwon sanyi, da kuma yadda za a magance shi idan an kamu da shi.
Duk wata cuta Allah shi ne wanda ke saukar da ita. Haka kuma babu wata cuta da ya saukar a doron kasa ba tare da maganin ta ba.
Kalmar ‘Sanyi’ ba wata kalma ce bare ba ga Hausawan duk duniya. Kuma dauke take da ma’anoni da yawa.
Akwai sanyin mara: Wato ciwon sanyin da maza ke dauka sakamakon tarawa da mace — ko kuma tsohon mataccen maniyyi ya dankare musu a mararsu.
A wata ma’anar kuma, “Ciwon sanyi na maza shi kuma mafi akasarin lokuta ya kan sa namiji kurajen kan azzakari, kankancewar gaba, daukewar sha’awa, fitar farin ruwa daga kwarkwaron azzakari da sauransu.
A bangaren mata ma suna iya kamuwa da sanyin mara sakamakon tarawa da ake da su, da kuma taruwar mataccen maniyyi a mararsu.
Akwai sanyin Mata: Tabbas Ubangiji na matukar kaunarmu bisa sanya tsabta da ya yi a matsayin cikon addini.
Wasu matan na kallon tsabtace bandaki a matsayin aikin wahala, amma wallahi ba aikin wahala ba ne.
In ka shiga kauyuka da karkara, sai ka taras lalacewar lamarin ta yi kamarin da sai dai mu ce Allah shi sawaka.
Mata na kamuwa da ciwon sanyi infection ne sakamakon amfani da suke yi da kazamin bandaki, suna fitsari a wuri maras tsabta mai dauke da kwayoyin cuta.
“Sanyi infection na mata ciwo ne da ke sanya mace ta rinka kurajen gaba, ta na jin gabanta na kaikayi, ko gabanta ya na fidda farin ruwa mai wari, ko kuma ta na fama da matsalar rashin sha’awa ko rashin gamsuwa yayin da ake saduwa da ita da sauransu.”
Bisa wannan dalili ya zama wajibi duk wata mace wacce sanyi (infection) ya kama ta ta nemi magani domin samun waraka.
Alamomin sanyin mata: A turance dai ana kiran alamomin kowacce irin cuta da ‘symptoms’, to shi ma ciwon sanyin mata wato infection na da irin nasa alamomin.
Daga ciki akwai:
-
Ciwon mara mai tsanani
-
Daukewar sha’awa
-
Fitar jinin al’ada da wari baki-kirin
-
Kurajen gaba
-
Fitar wani ruwa mai wari daga gaban mace
-
Jin zafi yayin da ake tarawa da mace
-
Sannan yana hana haihuwa in ya yi karfi
Shi lalatar sanyin mata namiji zai iya kwasar sanyin daga wurin matarsa. Yayin da shi kansa namijin in yana fama da ciwon sanyin zai iya shafa wa matarsa.
Amma akwai wadansu abubuwa da ke kawo ciwon sanyi (infection) na mata, daga ciki akwai:
-
Yin fitsari a bandaki marar tsabta
-
Yin tsarki da ruwan zafi ko sanyi ya yi yawa
-
Jima’i da mai cutar (mace ko namiji)
-
Sai cin danyar albasa.
Akwai hadin magungunan sanyi sosai, zan kawo wasu daga ciki masu kyau.
Maganin Sanyi I.
Wannan hadin maganin shi ne mafi sauki a cikin duk wasu hade-haden magungunan sanyi. An tabbatar da yana aiki sosai amma fa da yardar Allah.
A samu:
-
Ganyen zogale
-
Madara, nono, ko zuma
Yadda Ake Hada Shi
A nemi danyen ganyen zogale sai a dafa shi, in ya dahu sai ku mashe shi ku tace ruwan zogalen ku aje gefe.
Sai ku kawo maradarku, ko nono, ko zuma ku zuba a cikin ruwan zogalen ku shanye.
Amma fa ku debi ruwan yadda za ku iya shanyewa.
Ku cigaba da yin hadin nan kullum har tsawon sati daya zuwa biyu, da yardar Allah za a samu waraka.
Maganin Sanyi 2.
Shi ma dai wannan hadin maganin gargajiyar yana magance sanyi kowanne iri ne ga maza da mata.
Sannan mutum zai iya hada shi ya gwada ko da kuwa ba shi da lalurar sanyi.
Amma dai, duk gaggawar asara ai ta jirayi samu ko!
Domin hada shi, sai a nemi:
-
Man tafarnuwa
-
Danyar citta
-
Zuma
-
Khaltuffa
Yada Ake Hada Shi
Abu na farko da za ku fara yi shi ne ku samu tasa ku zuba ruwa kofi biyu a ciki, sai ku dora a wuta.
Daga nan sai ku samo cittarku manya guda biyu danya ku dake ta.
Ku debo dakakkiyar cittar ku zuba a cikin ruwan nan da ke kan wuta, ku bar ta ta tafasa sannan ku sauke.
Sai ku na tsiyayar ruwan cittar nan a kofi, kuna saka zuma cokali 8, da man tafarnuwa cokali 4, da khaltuffa shi ma cokali 5 kuna juyawa kuna sha.
Ku rinka yin hadin safe da yamma kuna sha har na wasu ‘yan kwanaki kamar biyar ko dai yadda ya sauwaka.
Da yardar Allah za a samu sauki.
MAGANIN CIWON SANYI (TOILET INFECTION)
Wanda sanyi ya yi wa kamun rashin tausayi ga hanyar waraka da izinin Allah
ABUBUWAN DA ZA A NEMA:
1- Tafarnuwa
2- Saiwar tumfafiya
3- Kananfari
4- Citta
5- Jar kanwa
YADDA ZA A HADA:
A samu saiwar tumfafiya ‘yar kadan sai a sara ta a wanke ta fes sai a hada da kanunfari da citta da tafarnuwa daidai sai a zuba ruwa Liter daya sai a sa jar kanwa kadan. Sai a dafa shi sosai.
YADDA ZA A SHA:
Za a dinga shan rabin kofi sau biyu a rana zuwa kwana 7.
TANBIHI.
Ana so a dinga sha da dumi sannan a dinga lura da kalar fitsari.
Wadannan kadan ne daga cikin magungunan da za a iya haɗawa a sha game da lalurar ciwon sanyi na mata da maza. Amma yana da kyau a dinga zuwa asibiti ana tuntubar likitoci game da lalurar.