Yaya ake wankan haila a musulunci? Nawa ne kwanakin wadda ta fara da kwanakin wadda ta saba?
Wankan haila wanka ne da ake yi bayan ɗaukewar jinin haila da mata suke yi a farko, tsakiya ko ƙarshen kowane wata, kawai dai ya danganta da lokacin da kowace mace take fara nata. Sannan wankan iri ɗaya ne da sauran wanka na tsarki, sai dai ya banbanta da niyya ne.
Yadda ake wankan shi ne: Da farko zaki fara wanke hannayenki kafin ki tsoma su a cikin ruwa, ki karkata abin da ruwanki ke ciki ta hanyar kwarara ma hannayenki ki wanke.
Sannan sai ki yi tsarki, ki wanke gabanki har zuwa cinyoyinki zuwa guiwarki.
Sannan ki yi alwalla, shuɗi ɗaya ko biyu ko ukku.
Sannan ki ɗebi ruwa ga hannunki ki yamutsa gashin kanki, saboda ƙofofin kanki su rufe.
Sannan sai ki wanke kanki gabaɗaya.
Sannan sai ki wanke ɓangaren jikinki na dama, sannan sai na haggu, sai ki kuma ki game jikinki da ruwa ki cigaba da cuccuɗawa.
Ki tabbatar da gashin kanki ya samu ruwa sosai, domin “A ƙasan kowane gashi akwai janaba”, kamar yadda Manzon Allah S.A.W ya ce.
Wannan itace Sigar wankan haila kamar yadda Hadis ya koyar da mu.
Sannan akwai wata sigar wadda da kin zo zaki cigaba da wanka, ki wanke ko’ina, ki cuccuɗa, ba tare da kin yi irin wancan na sama ba.
Kuma wankan Haila da na Janaba duk iri ɗaya ne, banbancinsu ita ce Niyya.
Da fatan Allah yayi mana jagoranci Amiin.