Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya ce akwai wasu mutane bakwai da zasu shiga a Inuwar Al’arshin Ubangijinmu a ranar tashin Alkiyama, ranar da babu wata inuwa sai ita.
Toh su waye Waɗannan mutanen?
Tabbas akwai wasu mutane guda bakwai wadanda za su shiga i uwar Al’arshin Ubangijinmu a ranar tashin alƙiyama, wadda wannan inuwa babu wata face ita. Waɗannan mutane kuwa suna cikin hadisin da Bukhari ya rawaito ne.
سبعة يظلهم الله في ظله يوم لا ظل إلا ظله: إمام عادل، وشاب نشأ في عبادة الله، ورجل قلبه معلق بالمساجد، ورجلان تحابا في الله اجتمعا عليه وتفرقا عليه، ورجل دعته امرأة ذات منصب وجمال فقال: إني أخاف الله، ورجل تصدق بصدقة فأخفاها حتى لا تعلم شماله ما تنفق يمينه، ورجل ذكر الله خاليًا
1- Shugaba adali
2- Matashin da ya taso cikin ibadar Allah
3- Mutumin da zuciyarsa take ɗamfare da masallaci.
4- Mutane biyun da suke son junansu saboda Allah, suka yi tarayya saboda Allah, kuma suka rabu saboda Allah.
5- Mutumin da wata mace mai matsayi kuma kyakkyawa ta neme shi, amma sai ya ce mata “ina tsoron Allah”
6- Mutumin da ya yi sadaka a ɓoye, har hagunsa ma ba ta san abin da damansa ta ciyar ba.
7- Mutumin da ya tuna Allah shi kaɗai, kuma ya zubar da hawaye.
Waɗannan su ne mutane bakwai da za su shiga i uwar Al’arshin Ubangijinmu a ranar da babu wata inuwa sai ita.
WALLAHU TA’ALA A’ALAM.
Masha Allah, Allah ya saka da Alkhairi Amiin