Menene hukuncin yin alwala ko wankan ibada da ruwan zafi a lokacin sanyi?
Sannan akwai banbancin lada tsakanin wanda ya yi wanka ko alwala da ruwan zafi, da kuma wanda ya yi da ruwan sanyi a lokacin hunturu?
Rangwamen da Addini ya yi mana yayin alwala ko wankan ibada a lokacin sanyin hunturu.
Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai.
Kamar dai yadda muka sani, yanzu lokacin sanyi ne muna cikinsa gadan-gadan. Wato shi sanyi yana da wasu darajoji da muhimman lokuta a cikinsa,saboda haka kada mu yi wasa da ibada a cikinsa, kuma kada mu aibanta zuwansa.
FALALAR LOKACIN SANYI:
“Annabi ﷺ ya ce shin ba na nuna muku Abin da Allah yake Kankare Zunubai da shi ba, kuma yake daukaka darajar bawa da shi, (sahabbai suka ce eh,) sai ya ce cika alwala a lokacin sanyi (lokacin da mutum yake kyamar taba ruwa) da yawan tattaki zuwa masallaci, da zaman jiran lokacin sallah, wannan shi ne ribaɗi wannan shine ribaɗi (dako / tsammani)”
(Muslim da Tirmiziy)
GARAƁASAR LOKACIN SANYI:
Manzon Allah ﷺ, Yace:
“Shin ba na nuna muku Abin da Allah yake Kankare Zunubai da shi ba, kuma yake kara muku lada, (sai sahabbai suka ce eh,) sai yace cika alwala a lokacin da jiki ba ya so, da yawan tattaki izuwa masallaci, wannan shi ne ribaɗi wannan shi ne ribaɗi”
(Muslim)
DARAJAR LOKACIN SANYI:
Umar Ɗan Kaɗɗabi ya ce:
Lokacin sanyi wata ganima ta masu bautar Allah, (ma’ana bayi za su yawaita yin azumi cikin sauƙi, da ƙiyamul-lali cikin dare.
(Al-Hilyatu Abu Nu’aim)
Amir Ɗan Ma’sud Yace:
Lokacin Sanyi wata ganima ce wacce ta zo a araha.
(Musnad Imamu Ahmad)
IBADA A LOKACIN SANYI:
Hasanul-Basariy Yace:
Lokacin sanyi zamini ne na mumini, yininsa ba shi da tsawo, sai ya yi azumi a cikinsa, darensa kuma dogo ne, sai yai ta yin ƙiyamul-lali (sallar dare)
Daga cikin rangwamen da Addini ya yi a lokacin hunturu, akwai Amfani da ruwan zafi wajen wanka da tsaftace
jiki. Domin ba jarumta ba ne
yin amfani da ruwa mai
tsananin sanyi lokacin
sanyi domin yana iya
janyo wa mutum rashin
lafiya. Addinin ya zo da kare
lafiya da ran mutum.
Allah ya ce:
[ ﻭﻻ ﺗﻠﻘﻮﺍ ﺑﺄﻳﺪﻳﻜﻢ ﺇﻟﻰ ﺍﻟﺘﻬﻠﻜﺔ]☆
Kuma ya ce:
[ ﻭﻻ ﺗﻘﺘﻠﻮﺍ ﺃﻧﻔﺴﻜﻢ ﺍﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﻛﺎﻥ
ﺑﻜﻢ ﺭﺣﻴﻤﺎ]☆
Ya zo a hadisi ce wa wasu
sahabbai sun yi fatawa ga
wani d’an’uwansu da
janaba ta same shi alokacin
sanyi.
Kuma suna matafiya,
kuma ba shi da lafiya.
Da ya yi wanka da ruwan
sanyi sai ya mutu, da suka
dawo suka fada wa
Manzon Allah sallallahu
alaihi wa sallam sai ya ce:
(ﻗﺘﻠﻮﻩ ﻗﺘﻠﻬﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻻ ﺳﺄﻟﻮﺍ
ﺣﻴﻦ ﺟﻬﻠﻮﺍ ﻓﺎﻧﻤﺎ ﺷﻔﺎﺀ ﺍﻟﻌﻲ
ﺍﻟﺴﺆﺍﻝ )
KYAUTATA ALWALA DA
CIKA TA, KOMAI TSANANIN
SANYI,
saboda hadisin da Muslim
ya rawaito.
ﻋﻦ ﺃﺑﻲ ﻫﺮﻳﺮﺓ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ
ﺃﻥ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ
ﻭﺳﻠﻢ ﻗﺎﻝ” ﺃﻻ ﺃﺩﻟﻜﻢ ﻋﻠﻰ ﻣﺎ
ﻳﻤﺤﻮ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﻪ ﺍﻟﺨﻄﺎﻳﺎ ﻭﻳﺮﻓﻊ ﺑﻪ
ﺍﻟﺪﺭﺟﺎﺕ: ﻗﺎﻟﻮﺍ: ﺑﻠﻰ ﻳﺎ ﺭﺳﻮﻝ
ﺍﻟﻠﻪ ﻗﺎﻝ: ﺇﺳﺒﺎﻍ ﺍﻟﻮﺿﻮﺀ ﻋﻠﻰ
ﺍﻟﻤﻜﺎﺭﻩ، ﻭﻛﺜﺮﺓ ﺍﻟﺨﻄﺎ ﺇﻟﻰ
ﺍﻟﻤﺴﺎﺟﺪ ﻭﺍﻧﺘﻈﺎﺭ ﺍﻟﺼﻼﺓ ﺑﻌﺪ
ﺍﻟﺼﻼﺓ، ﻓﺬﻟﻜﻢ ﺍﻟﺮﺑﺎﻁ ﻓﺬﻟﻜﻢ
ﺍﻟﺮﺑﺎﻁ ”
ﺭﻭﺍﻩ ﻣﺴﻠﻢ.
Manzon Allah sallallahu
alaihi wa sallam ya ce:
Shin ba zan fada muku
abin da Allah yake shafe
kurakurai da shi ba, kuma
yake daga darajoji da shi?
Suka ce eh ya manzon
Allah.
Sai yace:
CIKA ALWALA TARE DA
SAMUN ABABEN DA ZA SU
SA YIN HAKAN.
ﻗﺎﻝ ﺍﻟﻨﻮﻭﻱ ﻓﻲ ﺷﺮﺡ ﻣﺴﻠﻢ:
ﻭﺇﺳﺒﺎﻍ ﺍﻟﻮﺿﻮﺀ ﺇﺗﻤﺎﻣﻪ ،
ﻭﺍﻟﻤﻜﺎﺭﻩ ﺗﻜﻮﻥ ﺑﺸﺪﺓ ﺍﻟﺒﺮﺩ ﻭﺃﻟﻢ
ﺍﻟﺠﺴﻢ ﻭﻧﺤﻮ ﺫﻟﻚ. ﺍﻧﺘﻬﻰ .
KIYAYE SALLAR ASUBA
CIKIN JAM’I
hadisai da yawa sun zo suna
tsoratarwa kan Rashin
halartar Asuba da Isha a jam’i.
Har Manzon Allah ya ce
su ne suka fi nauyi ga
munafukai, ka yi kokari ya
kai bawan allah ka ceci
kanka daga fada wa gungun
muafukai da barin sallar
Asuba a lokacin sanyi domin
ba ka san sanda mutuwa
za ta zo maka ba.
Haka nan hadisai sun zo
suna bushara ga masu
kiyeye sallar Asuba a
lokacinta cikin jam’i,
malamai suka ce
wadannan hadisai sun
kunshi kusan busharori
goma ga masu kiyaye ta.
RAYA SUNNAR SHAFA
KAN HUFFI KO SAFA:
Lalle shafa kan huffi ko
safa ya halatta ga matafiyi
da wanda ke zaune a gida,
idan ya saka huffi ko safa
lokacin da ya yi alwala ya yi
niyyar shafa kansu, duk
lokacin da zai jaddada
alwala,
Kwana daya da yini ga
mazaunin gida,kwana
uku ga matafiyi.
Matukar mutum bai
kwabe su ba a cikin wannan
lokacin to lalle zai iya
shafa a kansu.
Wannan yana daga cikin
sassaucin shari’a da rage
damuwa, musamman
lokacin sanyi da ake
yawan saka huffi da safa,
cirewa da sawa akwai
damuwa ga mutum, sai Allah
ya dage wannan damuwar
da shafa kan huffi da safa,
ya kayyade lokaci na
hakan domin kiyaye tsafta,
wannan yana daga cikin
ababe masu kayatarwa a
addini.
TANADAR ABIN
DUMAMA RUWA GA MASU
AURE DA GWAGWARE:
saboda mai aure idan ya
sadu da iyali zai bukaci
ruwan zafi, idan ba shi da
abin dumamawa sallah da
alkairai da yawa za su iya
kubuce masa, musamman
da daddare.
Haka nan yawan mafarke-
mafarke yana faruwa ga
gwagware lokacin sanyi
musamman da dare, sai
hakan ya sa suna rasa
sallah a kan lokacin ta,
saboda ga sanyi babu abin
dumama ruwa, abin da ya
kamata shi ne mutum ya
samu abin da zai rika
taskance ruwan zafi da shi.
Domin yin amfani da shi
idan ya bukata.
WASU HUKUNCE-
HUKUNCE DA YA KEBANCI
LOKACIN SANYI:
1: Hada sallah biyu kamar
azahar da la’asar da isha
da asuba, saboda sanyi mai
tsanani tare da iska.
2: Yin sallar nafila kan
abun hawa dabbace ko
mota.
3: Yin addu’a lokacin da iska
ta taso,
{ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺇﻧﻲ ﺃﺳﺄﻟﻚ ﺧﻴﺮﻫﺎ ﻭﺧﻴﺮ
ﻣﺎ ﺃﺭﺳﻠﺖ ﺑﻪ، ﻭﺃﻋﻮﺫ ﺑﻚ ﻣﻦ
ﺷﺮﻫﺎ ﻭﺷﺮ ﻣﺎ ﺃﺭﺳﻠﺖ ﺑﻪ }.
Wannan kadan ne daga cikin irin rangwamen da Addini ya zo da shi a lokacin sanyin hunturu.