Yaya tunanin Bahaushe yake game da tsarin ƙayyade iyali a yau.
A mafi yawancin lokutta, Bahaushe yana kallon wasu al’amura ne da irin fuskar da addinin Musulunci yake kallon abin, domin mafi yawan Hausawa Musulmai ne, kuma suna bin addini sau da ƙafa, kuma dai-dai iyawarsu.
Don haka ne ma a fuskar Ƙayyade iyali ba kowane Bahaushe ne ke da ra’ayin kansa ba, duk da dama rayuwa ba wai ra’ayi ce ba. Kuma tunda haka ne, dole ne mu koma mu ga me addini ya ce game da ƙayyade iyali, sai mu yi comparison mu ga idan ya yi dai-dai da ra’ayin Bahaushe a yau.
Addinin Musulunci ya kalli tsarin iyali ta fuska biyu, wato Halal da Haram, don haka a nan ma sai mun ji ta ina haram ɗin take, sannan ta ina yake zama halal?
Dalilan da suke sa tsarin iyali ya zama haram ta fuskar addini sun haɗa da:
1. Tsoron talauci.
2. Koyi da turawa.
3. Tilastawar hukuma.
4. Ƙauracema haihuwa gabaɗaya.
5. Yin tsarin iyalin ba tare da amincewar miji ba.
Waɗannan su ne dalilan da tsarin iyali ya haramta ta fuskar addini, don haka mafiya yawan hausawa sun tafi a kan haka, sai waɗanda ba za’a rasa ba.
A bangaren da addini ya halasta Ƙayyade iyali kuma akwai:
1. Lalura.
2. Domin lafiyar Uwa, da ɗanta.
3. Abin da ya shafi matsalar mahaifa.
4. Abin da ya shafi cutar gado, misalin Sikla d.s.
Waɗannan ɓangarorin ne addini ya halasta Ƙayyade iyali, kuma duk wani bahaushen da zaka tambaya dalilinsa na Ƙayyade iyali, zai kawo maka ɗaya daga cikin waɗannan.
Wannan ne ke nuna Bahaushe yana yin tsarin iyali ko ƙin yi ne bisa ga kyakkyawar fahimtar da ya yi ma addininsa.
Duk da akwai waɗanda suke ƙin ƙayyade iyali bisa ga wani ra’yinsu na daban, ko don gasar tara yara tsakanin kishiyoyi, ko kuma kawai rashin hujja saboda ƙarancin ilimi.
Amma dai a wannan lokacin da muke ciki, Bahaushe ya karɓi Ƙayyade iyali ɗari bisa dari, dai-dai da fahimtar da addinin Musulunci ya yi ma tsarin iyalin.