Kamar yadda aka ce zato zunubi ne ko da ya kasance gaskiya. Ina son sanin illar munana zato ga mutane a musulunci.
Addinin musulunci ya umarci Musulmi da su yi wa junansu kyakkyawan zato kuma su yi wa ayyukan mumini kyakkyawar fassara wadda ta dace da shari’a. Bai halatta ba wani ya ɗauka cewa “wane fasiqi ne.” matuqar bai tabbatar da ƙaƙƙarfar hujja ba.
Imam Ali (AS) yace:
“Ka ɗauki al’amarin ɗan uwanka a matsayi mafi kyau har sai wani abu da zai sa ka janye ya bayyana a gare ka, ka da ka yi mummunan zato ga kalmar da ta fito daga bakin ɗan uwanka alhali za ka iya yi mata kyakkyawan zato.”
Yi wa juna kyakkyawan zato yana ƙulla ƙauna a tsakanin jama’a kuma ya samar da haɗin kai a tsakanin su. Shugabannin musulunci sun yi bayanai iri-iri dangane da sakamakon kyakkyawan zato. Imam Ali (AS) yana cewa:
“Duk wanda ya yi kyakkyawan zato wa mutane to za su so shi.”
Littafin Gurarul Hikam
Dokta Marden yace:
“Idan za ku yi abota da wani, to ku yi ƙoƙari ku dubi kyawawan halayen sa da ɗabi’un sa na ƙwarai kawai. Sa’annan kuma kuyi ƙoƙari ku mutunta waɗannan halaye nasa a zuciyar ku. Idan har kuka yarda da wannan wasiyya tawa kuka riƙe ta a zuciyar ku to za ku yi zaman lafiya da kowa kuma kowa zai yi sha’awar ƙulla abota da ku.”
Kyakkyawan zato da amincewa da jama’a na iya canja hatta tunanin wadanda suka dulmiye a cikin zunubi ma. Yazo a littafin Gurarul Hikam shafi na 378 cewa Imam Ali (AS) yana cewa:
“Kyakkyawan zato yana kuɓutar da wanda ya dulmiya a cikin aikata zunubi.”
Imam Ali (AS) yana cewa:
“Kyakkyawan zato hutun zuciya ne kuma kubutar addini ne.”
Littafin Gurarul Hikam shafi na 376
Kyakkyawan zato magani ne mai warke zulumin al’amuran rayuwa na yau da kullum. Ya zo a littafin Gurarul Hikam shafi na 377 cewa Imam ali (AS) yana cewa: “Kyakkyawan zato na rage zalama”.
Dr. Marden na cewa:
“Babu wani abu da zai sa mu ga kyawun rayuwa kuma ya rage mana ɗacin ta, ya buɗa mana hanyar muwafaƙa kamar kyakkyawan zato. Ku ji tsoron mummunan zato kamar yadda ku ke tsoron cututtuka da jafa’i. Ku bude ƙwaƙwalwar ku ga kyakkyawan zato za ku yi al’ajabin yadda za ku tsira daga munanan tunane-tunane cikin sauƙi”.
Lalle ne mu’amalar musulmi ta zamo ta yi nesa da mugun fata da mummunan zato a tsakanin su. Dan hakane Imam Ali (AS) yake wasici, inda yake cewa a kyautata mu’amala a tsakanin juna. Matuƙar jama’a suna yi maka kyakkyawan zato; to kada ka aikata abin da zai sa su ga tsiraicin ka har ka basu kunya.
“Duk wanda ya dogara da kai yana maka tsammanin alheri to lalle yayi maka kyakkyawan zato, dan haka kada ka sabawa zaton sa”.