Mene ne bambancin tsakanin maganin da malami zai yi da wanda boka zai yi wajen warkar da ciwo?
Banbanci tsakanin maganin da Malami zai yi, da wanda boka zai yi a bayyane yake. Sai dai kafin nan yana da kyau mu san waye Malami? Sannan waya Boka.?
Malami:- A harkar bada magani, shi ne wanda yake ba da magunguna bisa ga koyarwar Al-qur’ani da Sunnah, da kuma kimiyyar musulunci. Duk irin maganin da zai bada ba zai wuce wannan bangarorin ba. Daga cikin nau’aukan magungunan da yake bayarwa a kwai irinsu Ruƙiyya, da kuma haɗe-haɗen magunguna irinsu Zaitun, habbatu ssaudah, karkar, kal tuffah d.s. Dukkan wadannan magungunan sun samo asali ne daga koyarwar Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama, inda ake haɗa su ta fuskoki daban-daban, wurin warkar da mabanbantan cutuka.
Malam Duba (Malamin Tsibbu):- Shi kuma Malami ne mai fuska biyu, yana bada magani ne da Alkur’ani, haɗe da bugun ƙasa (Duba). Sannan kuma da wasu laƙunƙuna wanda gargajiya ta zo da su. Shi ya kan sauya wasu ayoyi na Alkur’ani, ta hanyar ƙara musu wani abu. Misali, inda zai ce a buɗe harafin “Minjaye” a saka sunan mutum, don mallaka ko wani abu na daban.
Boka:- Shi ne wanda ya ke aiki da aljannu wurin magungunansa, sannan shi ya kafurce ma Allah da Manzonsa, kuma duk wanda ya je wurinsa ya yi shirka, saboda yana da’awar sanin gaibu, da kuma yin abin da Allah ne kaɗai yake yi ma bayinsa, kamar azurtawa da sauransu.
Idan muka yi duba da ma’anar kowannen su, zamu iya gane banbancin da ke tsakanin su. Dukkanin su magunguna suke haɗawa su bada, kuma idan Allah ya nufa ana samun lafiya. Sa dai halaccin zuwa wurinsu ne Musulunci ya ware.
Malami mai bada magani da Alkur’ani da kuma koyarwar Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ne kaɗai addini ya yarda da je wurinsa cikin waɗannan ukun, kuma an fi samun waraka wadda babu cuta babu cutarwa a cikinta.
Amma waɗancan biyun, wato Malamin duba, da boka, Musulunci bai yarda da zuwa wurinsu ba, saboda duk sun saɓa ma koyarwar Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama. Kuma magungunansu akwai cuta da cutarwa a ciki, sai mu yi fatan Allah ya tsare mana Imaninmu, ya kuma ƙara mana lafiya Amiiin.