MENE NE BAMBANCIN RAYUWA KAFIN MUTUWA, DA KUMA RAYUWA BAYAN MUTUWA?
Rayuwa kafin mutuwa tana farawa ne tun daga ranar da aka haifi mutum, har ya zuwa ranar da zai koma ma mahaliccinsa. La’alla rayuwar ta yi tsawo ne, ko kuma bata yi ba, sannan rayuwar da lafiya ne ko babu. Kuma babbar manufar rayuwar ita ce a bauta ma Allah, domin don haka ne Allah ya halicce mu, kamar yadda ya faɗa a littafinsa mai tsarki, cewar “Ban halicci Mutum da Aljani ba sai don su bauta Mani”, wannan ayar ta tabbatar mana da manufar rayuwarmu kafin mutuwa ita ce, domin mu bauta ma Allah, mu kasance masu ɗa’a ga umurni ko haninsa a kanmu, wanda Manzonsa Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama ya zo mana da shi. Ta haka ne zamu ci riba a rayuwarmu da zata zo bayan mutuwa.
Rayuwa bayan mutuwa tana farawa ne daga lokacin da aka zare ma mutum ransa, sannan tana cigaba da tafiya ne daga kwanciyar ƙabari, inda a nan ne bawa zai fara girbar abin da ya shuka, na Alkhairi ne ko na sharri. Idan mutum mumini ne zai samu rayuwar ƙabari mai cike da ni’ima da nutsuwa, idan kuma fajiri ne, toh zai riski rayuwar cikin ƙabari mai ƙunci da bala’i da musiba. Daga kwanciyar ƙabari ne kuma idan aka tashi ta hanyar busa ta biyu, wato tashin Alkiyama, za a dasa wata rayuwar wadda take cigaban rayuwa bayan mutuwa.
Ranar tashin Alkiyama ne kuma wata rayuwa mai cike da ruɗu da firgici zata dasa, inda kowa sai ya ji a jikinsa a wannan rana, saboda babu wanda ya san makomarsa tsakanin wuta da Aljanna, har sai lokacin da Allah ya so mu da rahama, har aka fara ceto da kuma rarraba sakamako. Daga nan ne ƴan wuta zasu tafi wuta, ƴan aljanna ma zasu tafi aljanna, anan ne kuma za a dasa rayuwa mai dauwama wadda bata yankewa, wasu zasu dauwama cikin farinciki sakamakon rahamar Allah, da kuma kyawawan ayyukansu. Wasu kuma zasu dauwama a cikin azaba, sakamakon munanan ayyukansu na saɓon Allah.
Allah ka sa mu yi kyakkyawan karshe, sannan ka yi mana kyakkyawar makoma Amiiiiin.