Watanni nawa matar da mijinta ya mutu take ɗebewa wajen yin takaba?
Da fari dai takaba ita ce zaman da mace za ta yi bayan rasuwar maigidanta na wadansu kwanuka sanannu, ba tare da ado dakwalliya ba, ba kuma da yin wani auren ba, ko yi wa wani alkawari, ko sanya dukkan abin da zai ja hankalin wani, na tufafi ko kayan karau.
Matar da za ta yi zaman takaba, ita ce dukkan matar da mijinta ya riga mu gidan gaskiya, tana matarshi, sun yi saduwar aure ko ba su yi ba, muddin akwai igiyar aure a tsakanin su, to za ta yi takaba. Misali (Allah ya kiyaye) idan aka daura auren mutum da karfe 2:30 na rana, sannan bayan minti 30 ko awa guda ya rasu, to fa takaba ta hau kanta, kuma za ta ci gadon shi, domin matar shi ce. Kamar yadda Abdullahi Dan Mas’ud Allah ya kara masa yarda, ya ba da amsa a lokacin da aka tambaye shi, aka ce da shi:
“Mutum ne ya auri mace amma bai bayyana mata sadakinta ba, kuma bai sadu da ita ba har ya rasu?”
Sai Dan Mas’udin ya ce. “Zan bada amsa da fahimtata, idan na yi daidai to daga Allah ne, idan kuwa ban yi daidai ba to daga Shaidan ne, Allah da Ma’aikin Shi sun barranta da wannan amsar. Tana da sadakin mata ire-irenta,ba kari ba ragi, kuma za ta yi takaba, sannan tana da gado.”
Sai Ma’akil Dan Sinan wanda yake daga kabilar Ashja’a ya mike yace:
“Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya yi irin wannan hukuncin da ka yi ga Rauh Diyar Washik –wata mace ce daga cikin mu.”
Sai Abdullahi Dan Mas’ud ya yi farinciki da wannan Magana tasa. Imam Ahmad da Abu-Daud da Tirmizi da Nasa’i da Ibnu Majah suka ruwaito wannan hadisin, kuma Tirmizi ya Inganta shi.
Haka nan kuma in da mutum zai rabu da mai dakinsa da saki daya ko biyu, sannan ya rasu kafin ta kammala iddar saki, shi kenan sai ta koma takaba, matarshi ce yana da dama ya dawo da ita a koyaushe muddin ba ta kammala idda ba.
Gwargwadon kwanakin Takaba:
Alokacin da mutum ya rasu, to zai bar iyalin shi a dayan halaye biyu, ko dai ta zama tana da Juna biyu ko kuma ba ta da shi. Idan ba ta da juna biyu to takabarta ita ce wata hudu da kwana goma.
Kamar yadda Allah Ya ce a cikin Suratul-Bakara.
“Kuma dukkanin mazan da ke rasuwa daga cikin ku su bar matansu, to matan za su zauna wata hudu da kwana goma.” Aya ta:234.
To amma idan ya rasu ya bar ta da juna biyu, a wannan lokacin karshen takabarta shine ta sauke abin da take dauke da shi, ko da ko ranar da ya rasu ne. Misali ya rasu 7:00 na safe ita kuma ta haihu 7:10 na safiyar, shi kenan ta kammala takabarta, idan wani ya gani ya ce yana so aka daura aure 2:30 na ranar aure ya dauru, dalili kuwa shi ne. fadin Allah a cikin Suratut-Talak.
“Kuma dukkanin mata masu juna biyu to lokacin su shi ne su sauke abin da suke dauke da shi.”
Haka kuma idan ya rasu ya bar ta da juna biyu na kimanin wata daya ko ma bai kai haka ba, to fa sai ta haihu, ka ga wannan takabarta na neman wata tara ko ma fiye kenan domin dai sai ta sauka. Zai iya yiwuwa a lokacin da maigida ya rasu ba ta san ma tana da juna biyu ba, wata kila a saduwar da bai wuce masa saura minti 30 a duniya ba ta samu juna biyun, to wannan za ta fara lissafin kwanaki ne na takaba sai daga baya takabarta ta koma sauraran haihuwa. Wannan ya nuna mana cewa mutum zai iya rasuwa ya bar matanshi biyu ko fiye da haka, amma wata ta riga wata kammala takaba, domin musulunci bai yarda a dauki dan wani gida a kai wani gida ba, wannan fa ko da mace mai takaba ta samu kwanciyar ciki, domin ciki yakan kai shekara 4 ko 6 kamar yadda malamai suka yi bayani, duba Tafsirin Adhwa’ul. Bayan Suratur-Ra’ad aya ta 8.
Abin da ake nufi da ta sauka shi ne, ta sauke duk abin da ke cikinta, ya zo da rai ko bai zo da rai ba, saboda haka ko bari ta yi ta kammala idda ko takaba idan aka samu shaidu a kan hakan, koma a ce siffar mutun ta bayyana a tare da shi barin, idan mai takaba ta haihu, sannan ingantaccen bincike ya nuna cewa tana dauke da ‘ya’ya biyu ne kuma ga shi ta haifi daya, to fa ba ta kammala ba sai ta haifi na biyun, domin abin da ake bukata ta sauke duk abin da take dauke da shi.
Yaushe za a fara lissafin Takaba?
Za a fara lissafin maitakaba ne daga lokacin da maigida ya rasu. Saboda haka daga ranar da mijinta ya rasu daga ranar ta fara idda, yana rasuwa ta shiga takaba.
Saboda haka Malamai sun yi maganganu biyu, idan ya rasu ba ta samu labarin rasuwar shi ba, sai bayan wata hudu da kwana goma, ko bayan haihuwarta sannan ta samu labarin shi kenan ta kamala takabarta.
Magana ta biyu kuma shi ne za ta fara lissafi daga ranar da labari ya zo mata, in kuma bayan wata biyu ne da rasuwar shi ta samu labarin rasuwar shi.
Me ya haramta ga maitakaba?
A dunkule abin da ya haramta ga maitakaba shi ne ado da kwalliya, da kuma yin aure ko yi wa wania alkawari, ko fita ba tare da wani dalili na Shari’a ba.
Yana da kyau mu bambance tsakanin kwalliya da tsafta, ya haramta ta yi kwalliya da ado, kamar sa tozali, kunshi, sa hoda, yin dizayin janfarce, janlebe, sanya tufafi na ado, sa turare in dai ba bayan ta kammala al’ada ta diga shi a kyalle domin ta sa a gabanta saboda rage karnin jini ba, da dai dukkan wani nau’i na ado ko kwalliya.
Amma ita tsafta babu wanda ya hana maitakaba yin ta, yin wanka kullum, yin kitso idan bukatar hakan ta taso ba kuma a yi don kwalliya ba, kuma ya halatta ta yi wanki domin duk suna cikin tsafta, sannan ya halatta ta share dakinta ba ta zauna kamar wata mai hauka ba.
Wallahu Ta’ala A’alam.