Wane irin kuskure mutum zai yi a cikin sallah har hukuncin Sujuda Ƙabli ko ba’adi ya sauka a kansa?
Sujuda Ƙabli da Sujuda Ba’adi su ne sujjadar rafkanuwa a cikin Sallah. Wato idan mutum ya yi shakka a cikin sallarsa to sai ya yi sujjadai guda biyu kafin sallama ko bayan sallama. In ko ya manta da sujjadar har lokaci ya yi tsawo, to sujjadar ta faɗi.
YADDA AKE YIN SUJJADAR QABLI DA SUJJADAR BA’ADI.
1- Sujjada Qabli : Ana yin ta ne kafin sallama. Bayan mutum ya yi tahiya, kafin ya yi sallama, sai ya sake yin wasu sujudu guda biyu, sannan ya sake yin wata tahiyar, sai ya yi sallama. Wannan ita ce Sujjada Qabali.
Dalilan da suke sa wa a yi ta: Idan mutum ya yi ragi a cikin Sallarsa, ko kuma ya tauye wasu sunnoni karfafa guda biyu ko sama da haka. (a takaice kenan).
ﺑَـﺎﺏٌ ﻓِﻲ ﺍﻟﺴُّﺠُﻮﺩِ ﻗَﺒْﻞَ ﺍﻟﺴَّﻼَﻡِ
ﻭَﺃَﻣَّﺎ ﺍﻟﺴُّﺠُﻮﺩُ ﺍﻟْﻘَﺒْﻠِﻲُّ ﻓَﺴَﺒْﻌَﺔٌ :
ﻓَﻤَﻦْ ﻧَﺴِﻲَ ﺗَﻜْﺒِﻴﺮَﺗَﻴْﻦِ ﻓَﺄَﻛْﺜَﺮَ ﻏَﻴْﺮَ ﺗَﻜْﺒِﻴﺮَﺓِ ﺍْﻹِﺣْﺮَﺍﻡِ ﺳَﺠَﺪَ ﻗَﺒْﻞَ ﺍﻟﺴَّﻼَﻡِ، ﻭَﻣَﻦْ ﻧَﺴِﻲَ ﺳَﻤِﻊَ ﺍﻟﻠﻪُ ﻟِﻤَﻦْ ﺣَﻤِﺪَﻩُ ﻣَﺮَّﺗَﻴْﻦِ ﻓَﺄَﻛْﺜَﺮَ ﺳَﺠَﺪَ ﻗَﺒْﻞَ ﺍﻟﺴَّﻼَﻡِ، ﻭَﻣَﻦْ ﻧَﺴِﻲَ ﺍﻟْﺠَﻠْﺴَﺔَ ﺍﻟْﻮُﺳْﻄَﻰ ﺳَﺠَﺪَ ﻗَﺒْﻞَ ﺍﻟﺴَّﻼَﻡِ، ﻭَﻣَﻦْ ﻧَﺴِﻲَ ﺍَﻟﺘَّﺸَﻬُّﺪَ ﺳَﺠَﺪَ ﻗَﺒْﻞَ ﺍﻟﺴَّﻼَﻡِ، ﻭَﻣَﻦْ ﻧَﻘَﺺَ ﻭَﺯَﺍﺩَ ﺳَﺠَﺪَ ﻗَﺒْﻞَ ﺍﻟﺴَّﻼَﻡِ، ﻭَﻣَﻦْ ﺃَﺳَﺮَّ ﻓِﻴﻤَﺎ ﻳُﺠْﻬَﺮُ ﻓِﻴﻪِ ﺳَﺠَﺪَ ﻗَﺒْﻞَ ﺍﻟﺴَّﻼَﻡِ .
ﺍِﻧْﺘَﻬَﻰ ﺍﻟﺴُّﺠُﻮﺩُ ﺍﻟْﻘَﺒْﻠِﻲُّ .
BABIN SUJJADA KAFIN SALLAMA.
Amma Sujjadar Kabli guda bakwai ce: –
1_Wanda ya manta kabbara biyu ko fiye banda kabbarar harama sai ya yi sujjada kabli.
2_Wanda ya manta (faɗin) Sami’allahu liman hamidahu, sau biyu ko fiye ya yi sujjada kabli.
3_Wanda ya manta zaman (tahiya) tsakiya ya yi sujjada kabli.
4_ Wanda ya manta karatun tahiya ya yi sujjada kabli.
5_Wanda ya rage ya qara ya yi sujjada kabli.
6_Wanda ya asirce (karatu) a inda ake bayyana shi ya yi sujjada kabli.
Sujjada Qabli sun tuke
2- SUJJADA BA’ADI : Ana yin ta ne bayan an yi tahiya an yi sallama, sai a sake yin wasu sujudu guda biyu, sannan a yi tahiya a yi sallama.
Dalilan da ya sa ake yin ta: Ana yin ta ne duk yayin da aka kara wani abu a cikin Sallah. Ko kuma yayin da mutum ya mance da wata farillah, ko kuma rukuni daga cikin sallarsa. Bayan ya kawo wannan farillar da ya mance, to sai ya yi sujjada ba’adi.
ﺑَـﺎﺏٌ ﻓِﻲ ﺍ ﻟﺴُّﺠُﻮﺩِ ﺍﻟْﺒَﻌْﺪِﻱِّ :
ﻭَﺃَﻣَّﺎ ﺍﻟﺴُّﺠُﻮﺩُ ﺍﻟْﺒَﻌْﺪِﻱُّ ﻓَﺴَﺒْﻌَﺔٌ :
ﻭَﻣَﻦْ ﺗَﻜَﻠَّﻢَ ﺳَﺎﻫِﻴًﺎ ﺳَﺠَﺪَ ﺑَﻌْﺪَ ﺍﻟﺴَّﻼَﻡِ، ﻭَﻣَﻦْ ﺳَﻠَّﻢَ ﻣِﻦْ ﺭَﻛْﻌَﺘَﻴْﻦِ ﺳَﺠَﺪَ ﺑَﻌْﺪَ ﺍﻟﺴَّﻼَﻡِ، ﻭَﻣَﻦْ ﺯَﺍﺩَ ﺭَﻛْﻌَﺔً ﺃَﻭْ ﺭَﻛْﻌَﺘَﻴْﻦِ ﺳَﺠَﺪَ ﺑَﻌْﺪَ ﺍﻟﺴَّﻼَﻡِ، ﻭَﻣَﻦْ ﺍِﺳْﺘَﻨْﻜَﺤَﻪُ ﺍﻟﺸَّﻚُّ ﺳَﺠَﺪَ ﺑَﻌْﺪَ ﺍﻟﺴَّﻼَﻡِ، ﻭَﻣَﻦْ ﺟَﻬَﺮَ ﻓِﻴﻤَﺎ ﻳُﺴَﺮُّ ﻓِﻴﻪِ ﺳَﺠَﺪَ ﺑَﻌْﺪَ ﺍﻟﺴَّﻼَﻡِ، ﻭَﻣَﻦْ ﺟَﻠَﺲَ ﻓِﻲ ﺍﻟﺮَّﻛْﻌَﺔِ ﺍْﻷُﻭﻟَﻰ ﺳَﺠَﺪَ ﺑَﻌْﺪَ ﺍﻟﺴَّﻼَﻡِ .
ﺍِﻧْﺘَﻬَﻰ ﺍﻟﺴُّﺠُﻮﺩُ ﺍﻟْﺒَﻌْﺪِﻱُّ .
BABIN SUJJADA BAYAN SALLAMA.
Amma sujjada bayan sallama guda bakwai ce:
1_Wanda ya yi zance da mantuwa ya yi sujjada ba’adi.
2_Wanda ya yi sallama a raka’a ta biyu ya yi sujjada ba’adi.
3_Wanda ya kara raka’a ɗaya ko biyu ya yi sujjada ba’adi.
4_Wanda kokwanto ya aure shi ya yi sujjada ba’adi
5_ Wanda ya bayyana (karatu) a inda ake boyewa ya yi sujjada ba’adi
6_ Wanda ya zauna a raka’a ta farko ya yi sujjada ba’adi
Sujjada ba’adi sun tuke
Wallahu Ta’ala a’alam.