Zanga zanga dai abu ne da ke aukuwa lokaci bayan lokaci, amma me ya sa?
Dalilin da ya sa mutane suke yi ma Gwamnati zanga-zanga guda ɗaya ne, sai dai a cikin wannan dalilin ɗaya akwai ƴaƴan da yake tafe da su, wanda Kafin mu ji wannan dalili yana da kyau mu fara sanin ma’anar ita kanta Zanga-zangar, idan ya so daga baya sai mu fito da wannan dalili.
MECECE ZANGA-ZANGA?
Zanga-zanga na nufin, hannunka mai sanda da Al’ummah ke yi zuwa ga gwamnati, ta hanyar fitowa a kan tituna, suna riƙe da alluna masu ɗauke da rubutun da ke bayyana damuwarsu, bisa ga manufar neman a kawar musu da wannan damuwar, wanda haƙƙin hakan na rataye a wuyan gwamnatin da ke riƙe da madafun iko.
Zanga-zanga ta kasu gida biyu, akwai ZANGA-ZANGAR LUMANA (Sulhu da neman mafita), akwai kuma ta BORE (Nuna gajiyawa da kuma ƙin goyon baya.) Dukkan waɗannan nau’ukan Zanga-zangar suna da matuƙar alfanu idan an yi su yadda ya dace.
DALILIN DA YA SA MUTANE YIN ZANGA-ZANGA SHINE:
Neman ma kai mafita a cikin abin da ya sha musu kai, Zanga-zangar ta lumana ce ko kuma ta bore.
Misalin Zanga-zangar da ta faru kwanan nan a Nigeria kaɗai ya isa ya bayyana mana dalilin yin Zanga-zanga, domin mutane suna cikin mawuyacin halin rashin tsaro da kuma tsadar rayuwa. Hakan ya sa suka zaɓi fitowa domin kai kokensu ga Gwamnati, ko da Allah zai sa a samu sauƙi.
Sai dai lokuta da dama illarta ta fi alkhairinta yawa, saboda ta kan chanja salo daga neman mafita, zuwa assasuwar rigima, kamar dai yadda muka gani a kwanan nan, inda wasu suka rasa rayuka, wasu kuma suka rasa dukiya, ƙarshe kuma buƙata bata biya ba. Don haka yana da kyau mutane su tsarkake zukatansu kafin su tsiri Zanga-zanga, hakan zai sa idan ta yi ruwa, rijiya, idan kuma ta ƙi ruwa, masai!
Da fatan Allah ya kawo mana mafita ta Alkhairi a ƙasarmu Nigeria Amiiiiin.
Amin. Sannu da ƙoƙari