Idan aka ce so, ana nufin yarda, sadaukarwa, da kuma muradi ko kwaɗaituwar zuciya,
A wani bayanin kuma so ƙaddara ne ga zuciya, wadda ɗan adam bai zai iya hana ta faruwa a kansa ba, domin shi ne ke sarrafa kansa, kuma ta sarrafa ɗan adam ɗin.
Amma dai a taƙaice da an ce so, toh ana nufin kwaɗaituwa akan wani abu da ido ya gani, kuma yake son mallaka, wanda kuma zai iya faɗawa a kan abu mai rai ko marar rai.
Misalin so ga abu mai rai: Mutum zai iya son mutum ɗan’uwansa, sannan zai iya son dabba, tsuntsu ko ƙwaro, sannan shi irin wannan son, yana da nau’ukansa kamar haka.
So na tsakanin Iyaye da ƴaƴansu, shi ne kuma so na musamman, wanda Allah kaɗai ne ya san girmansa, sannan Allah da Manzonsa ne kaɗai ake yi ma soyayyar da ta wuce wannan, don haka babu wata soyayya da za a iya kwatanta wa da soyayyar da ke tsakanin iyaye da ƴansu. Musamman son da ya ke fitowa daga zuciyar Uwa, wannan na daban ne.
Son da mutum ke yi ma dabba ko tsuntsaye d.s: wannan wani so ne na daban shi ma da Allah ya halitta ma zuciya, domin Allah ya sanya wasu daga cikin dabbobi su zama ni’ima a garemu, domin kuma mu gamsu da wannan ni’imar, sai Allah ya sanya mana son su. Sannan su ma dabbobin ana samun masu son mutane. Gwargwadon yadda kake kyautata ma wata dabbar, gwargwadon son da zata yi maka.
Misalin so ga abu marar rai: Abubuwa mararsa rai su ma sun shiga sahun so, sai dai soyayyar ɓangare ɗaya, wadda mutum mai rai ke yin ta. Da zaran mutum ya ga abu, kuma ya birge shi, toh zai iya son sa, har kuma ya mallake shi idan da hali.
Sannan idan muka dawo batun SO ɗin baki ɗaya, toh shi ya game kowa, mai hankali da marar hankali, domin hatta mahaukaci ya san so, kuma yana nuna shi. Har ila yau, shi so lokkuta da dama yana yaɗo, ko kuma bunƙasa har ya koma ƙauna, idan ana kyautata ma mai yin sa, domin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya ce “Ita zuciya an gina ta ne a kan son mai kyautata mata”, don haka kyautatawa jigo ce babba da ke bunƙasa da so.
Idan muka dawo batun so, wanda ake nufi da soyayya: To ana nufin haɗuwar zukata biyu, waɗanda suka amince ma juna, har ta kai sun ji zasu iya rayuwa da junansu, wanda hakan ke faruwa tsakanin mace da namiji.
So abu ne mai sa farinciki da nishaɗi ga wanda ya yi dace da shi, musamman idan mutum ya kasance tare da wanda yake tsananin so, shi ya sa wasu ke masa iƙrari da “So aljannar duniya.”
Sai dai fa shi ma Shu’umin gaske ne, domin idan ya yi ɓarna, to gyaranta sai Allah.
Fatanmu Allah ya haɗa mu da masoya na gari Amiin.