A haƙiƙanin gaskiya babu wata riba da aka samu, sai ma dai faɗuwa ƙasa warwas da aka yi. Idan muka yi duba da cewa wannan zanga-zanga an yi ta ne domin a samu sauƙin rayuwa bisa tsananin da ake ciki, to amma abin tambayar an samu sauƙin? Amsar a bayyane take idan muka yi duba da abubuwan da suka faru. Saboda an sake dilmiya al’umma cikin halin ƙaƙanikayi, wasu sun mutu, wasu sun ji rauni, wasu sun ƙare a gidan yari, wasu kuma sun rasa jarinsu sakamakon dirar mikiyar da aka yi a kan kayan sana’ar su. Game da waɗanda aka yi zanga-zangar a kansu kuwa ko a jikinsu wai an tsikari kakkausa, ba su damu da halin da al’umma suka shiga ba, don haka tun da fari maganin kada a yi, kada a fara, amma tun da alƙalami ya riga ya bushe an yi to magana ta ƙare, sai dai mun sani zanga-zanga ba ta haifar da ɗa mai ido ba, haka nan ba a samu riba da yin ta ba.
Wace riba aka samu sakamakon zanga-zanga?
Muhammad Asiya Unselected an answer August 28, 2024